Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su (Hotuna)

Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su (Hotuna)

An sadaukar da ranar mata ta duniya ne don karramawa da taya matan duniya murnar nasarorin da suke samu a fannoni daban-daban na rayuwarsu a duniya. Ranar kuwa na jawo hankulan masu karfafawa mata guiwa dakuma masu rajin kare hakkin matan a duniya.

An fitar da ranar 8 ga kowannen watan Maris ne don murnar ranar mata ta duniya din. Mata daga addinai, kabilu da kuma al’adu daban-daban kan hadu don taya juna murna.

A don haka ne muka tattara takaitaccen tarihin mata 5 na Arewa wadanda ake yaba kwazonsu kuma suka sha gwagwarmaya.

1.Hajiya Gambo Sawaba

‘Yar siyasa ce kuma mai rajin kare hakkin mata wacce ta shahara a ayyukan alherin da suka hada da yaki kan nemawa matan arewa ‘yanci.

Mahaifinta dan asalin kasar Ghana ne inda mahaifiyarta kuwa ‘yarkabilar Nupe ce. Tun tana yarinya, ta saba fada da masu zalunci tare da tausayawa wadanad aka zalunta. Wannan halin ne kuwa ta tashi da shi kuma ya saka mata tausayin talakawa da kuma marasa lafiya.

Gambo ta shiga siyasa ne tun tana da shekaru 17, a lokacin jam’iyyar NPC a Arewa. Amma gambo ta shiga jam’iyyar adawa ne. Ta rassu tana da shekaru 71 a duniya, watan Oktoba na 2001.

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su
Source: Twitter

2. Aisha Buhari

Matar shugaban kasar Najeriya ce, Muhammadu Buhari. Aisha tayi suna wajen kare hakkin mata da kananan yara. Wannan ne kuma ya zama abinda ta fi assasawa a kai ko a 2015 yayin da mijinta ke neman kujerar shugabancin kasa.

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gumina zan more; in ji uwar da ta auri dan cikinta

3. Hadiza Bala Usman

Tsohuwar dalibar jami’ar Ahamadu Bello da ke Zaria ce inda ta samu digirinta na farko a fannin kasuwanci. Ta yi digirinta na biyu ne jami’ar Leeds da ke UK.

Kafin a zabeta a matsayin mace ta farko da ta shugabanci NPA, Hadiza Bala Usman ta yi aiki da BPE bayan da UNDP suka dau hayarta don zama mataimakiya ga ministan babban birnin tarayya a kan tabbatar da manayan aiyuka.

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su
Source: Depositphotos

4. Zainab Ahmed

It ace minstar kudin najeriya a halin yanzu. Ta karanta fannin aikin banki ne a makaranta. Ta zama ministan kudin Najeriya ne tun bayan murabsu din kemi Adeosun.

It ace tsohuwar karamar minister kasafi da tsarin kudin kasa. A sama da shekaru 30 da ta dauka tana aiki, ta yi aiki a manayan wurare da matakai na tarayyara kasar nan.

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su
Source: UGC

5. Saadiya Aminu

It ace babbar manajar urban Shelter Limited, kamfanin dillacin gaidaje da ya kai shekaru 25. Saadiya na da digiri a fannin tattalin arziki daga jami’ar Brunei kuma tana da digiri na biyu a fannin kudi daga jami’ar SOAS da ke London.

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su

Ranar mata ta duniya: Takaitaccen tarihin fitattun mata 5 da arewa ke alfahari da su
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel