Yanzu-yanzu: Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantun kasar kan Coronavirus

Yanzu-yanzu: Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantun kasar kan Coronavirus

A cikin matakan da take dauke wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus, Kasar Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantu da jami'o'in masarautar fari daga ranar Litinin har ila ma sha'a llahu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA ta sanar da cewa ma'aikatar Ilimin kasar ta sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Febrairu 2020.

Jawabin yace: "An yanke shawarar kulle dukkan makarantu ne saboda kyakkyawar soyayyar da shugabancin ke yiwa yaranta kan tsaronsu kuma za'a samar da wasu hanyoyin ilmantar da su daga gidajensu."

Ministan harkokin ilimin Saudiyya ya bada umurnin ilmantar da yara daga gidajensu ta hanyar na'urorin zamani.

Kawo yanzu, mutane 11 sun kamu da cutar a kasar ta Saudiyya.

KU KARANTA: Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai mata biyar, da wasu uku a jihar Niger

A ranar 5 ga Maris, Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin babban limami, Sheikh Abdur-Rahman As-Sudais ta kaddamar da feshi da tsaftace Mataaf na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona.

Mabiya addinin Islama a fadin duniya sun yi mamakin hakan inda da dama suka ce wannan shine karo na farko da zasu ga Masallacin Harami babu kowa.

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah da ziyarar Masallacin Annabi mai girma ga dukkan yan kasar da mazauna sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta dau matakin ne domin takaita yaduwar cutar a kasar mai alfarma.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta alanta cewa a mayarwa dukkan wadanda suka biya kudin Umrah kudadensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel