Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai mata biyar, da wasu uku a jihar Niger

Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai mata biyar, da wasu uku a jihar Niger

Yan bindiga sunyi garkuwa da wasu dalibai mata 5 ,malamar makaranta da masu gadi biyu a wata makarantar kwana ta kudi, a karamar hukumar Mariga dake jihar Niger.

Sunyi garkuwa da daliban ne a makarantar Tular dake Moruba.

Shugaban yan sandan jihar yace harin ya faru ne daren Lahadi, amma basu samu labari ba sai daren Talata.

A halin yanzu, Kwamishinan yan sandan, Adamu Usman, ya tura tawagar yan sanda da sojoji zuwa makarantar, dake karamar hukumar Mariga.

Bisa ga bayanin kwamishinan yan sandan, yan bindigan sunci sa'ar rashin yanar gizo mai kyau ne hakan ya jawo suka kai hari makarantar.

Yace an kara samar da wasu jami’an tsaro saboda tsaro daga makamancin wannan harin .

Yace "Mun tura da wasu yan sanda domin su san ta hanyar da zasu ceto mana su ba tare da an ji musu rauni ba”

Shugaban yan sandan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya ga katangar makarantar wanda a a ganinshi tana daya daga cikin abinda ya basu daman saukin kai harin.

Har ila yau, yayi kira ga jama’a dasu bada hadin kai akan sanarwa yan sanda muhimman bayanai domin taimaka musu wurin bincike.

KU KARANTA Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantun kasar kan Coronavirus

Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai mata biyar, da wasu uku a jihar Niger

Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai mata biyar, da wasu uku a jihar Niger
Source: Depositphotos

A bangare guda, Biyo bayan tsoro da aka shiga kan ci gaba da kai hare-hare da kisan bayin Allah da ake yi a jahar Benue, shugaban kungiyar matasan Tiv na kasa a ranar Asabar ya bukaci matasan Benue yan kabilar Tiv da su dauki matakin kare kansu daga yawan hare-hare da kashe-kashen da ake yi.

Baya ga haka, kungiyar ta ba makiyaya sa’o’i 48 su tattara su bar jahar sannan ta yi barazanar cewa duk wanda ya gani daga cikinsu bayan karewar wa’adin toh za ta kawar dashi nan take.

Zababben shugaban kungiyar na kasa, Mista Timothy Hembaor ya bayyana hakan a wani jawabi da ya bai wa manema labarai a Makurdi, babbar birnin jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel