NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2

NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2

Hukumar kula da harkokin kamfanonin sadarwa na kasa (NCC) ta sanar da cewa ta sake rufe wasu layukan waya (SIM) saboda rashin yi musu rijista ta hanyar da ya dace.

A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Dambatta, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa yanzu an rufe duk wani layin waya marar rijista na kamfanonin sadarwar da ke Najeriya, ya ce an rufe wasu layukan saboda rashin yi musu rijista bisa ka'ida.

A kwanakin baya ne ministan harkokin sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya umarci hukumar NCC ta rufe dukkan wasu layukan wayar hannu da basu da rijista ko kuma ba a yi musu rijista ta hanyar da ya kamata ba.

Bayan wannan umarni, rahotanni sun rawaito cewa Dakta Pantami ya sake bayyana cewa bai kamata mutum daya ya mallaki layukan waya fiye da uku ba, a saboda haka NCC za ta dauki mataki a kan 'yan Najeriya masu layukan waya fiye da uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel