Kungiyar Musulunci ta saka baki cikin rikicin Sanusi da hukumar rashawa ta Kano

Kungiyar Musulunci ta saka baki cikin rikicin Sanusi da hukumar rashawa ta Kano

- Wata kungiya ta bukaci Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya fuskanci tuhumar da ake masa na rashawa ya dena zule wa

- Kungiyar ta Muslim Youth League ta ce zargin da aka yi wa Sarkin babban lamari ne kuma ya kamata ya amsa tambayoyi domin ya wanke kansa

- Kungiyar ta nuna rashin jin dadin ta kan adadin zargin rashawar da ake yi wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Wata kungiyar Musulunci mai suna Muslim Youth League (MYL) ta yi kira ga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano Muhammad Sanusi II game da zargin rashawa da ake masa.

Kungiyar ta zargi Sarkin da sayar da wasu filaye ba bisa ka'ida ba mallakar masarautar da kudin su ya kai naira biliyan 2 kuma da karkatar da kudaden ta hanyar amfani da wasu kamfanoni domin amfanin kansa.

Kungiyar ta bayyana takaicin ta kan yadda ake yawan zargin Sarkin ta aikata rashawa.

Wata kungiyar musulunci ta saka baki cikin rikicin Sanusi da hukumar rashawa ta Kano
Wata kungiyar musulunci ta saka baki cikin rikicin Sanusi da hukumar rashawa ta Kano
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu bayan sun sha maganin kara armashin jima'i sun kwana suna zina

A cikin sakon da ta aike wa manema labarai a ranar Asabar 7 ga watan Maris, kungiyar ta nuna rashin jin dadin ta kan yadda zargin da ake masa ke shafar al'ummar musulmi a kasar.

Idan ba a manta ba, Kungiyar Yaki da Rashawa da sauraron kararrakin al'umma ta aike da gayyata ga Sarkin domin ya gurfana gabanta a ranar 9 ga watan Maris na 2020 ya amsa tambayoyi.

Sai dai Sarki Sanusi ya shigar da bukatarsa a babban kotun jihar Kano domin neman kotun ta tana hukumar ta rashawar bincikarsa.

A cewar kungiyar musuluncin, "Sarkin ya dena labewa ya tafi ya wanke sunansa. Ya dena gudu kamar kazar da ba ta da kai ya tafi ya fuskanci zargin da ake masa.

"Ya dena tursasa hukumar rashawar ta bayyana sunayen wadanda suka tsegunta musu bayanan sirri domin hakan ka iya cikas ga binciken.

"Sarkin ne ya zargi tsohon shugaban kasar mu da cin hanci yanzu shima ga shi an same shi da karkatar da kudaden al'umma. Ya rufa wa kansa asiri."

Asali: Legit.ng

Online view pixel