NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambisa (Hotuna)

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambisa (Hotuna)

- Sojojin Najeriya suna cigaba da samun nasara a yakin da su ke yi da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram

- Nasarar da sojojin suka samu na baya-bayan nan shine a ranar Alhamis 5 ga watan Maris inda sojojin suka yi ruwan bama-bamai a sansanin Alafa 'C' a dajin Sambisa

- Sojojin sun tarwatsa mafi yawancin gidajen da ke sansanin kana sun kashe 'yan ta'adan da ke cikin gidajen

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta ce harin bama-bamai na sama da ta kai ya lalata sansanin 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram a Alafa 'C' da ke dajin Sambisa a jihar Borno.

A sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a ta bakin Direktan Yada Labaran ta, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce rundunar Operation Decisive Edge ne suka kai wa 'yan ta'addan harin.

A cewarsa, an kai harin ne bayan an tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kafa sansani da dama inda suke amfani da shi suna bawa mayakan su horo kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Daramola ya ce, "Bama-baman da roka da jiragen yakin na sojojin saman suka harba sun lalata gidajen inda suka ragargaza gidaje da dama kana suka kashe 'yan ta'adda da dama da ke cikin gidajen."

Mai magana da yawun na NAF ya kuma yi bayanin cewa rundunar, "tare da hadin gwiwa da sauran sojojin kasa za su cigaba da yakin da suke yi na kokarin turnuko 'yan ta'addan daga mabuyarsu domin sauran sojojin da ke kasa su cigaba da yakar su."

Ga hotunan hare-haren da suka kai a kasa:

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)
Source: UGC

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu bayan sun sha maganin kara armashin jima'i sun kwana suna zina

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)
Source: UGC

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)
Source: UGC

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)

NAF ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan bama-bamai a dajin Sambia (Hotuna)
Source: UGC

Wannan na daya daga cikin nasarorin da sojojin suka samu a yakin da suke yi da 'yan ta'addan.

A kwana-kwanan gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya yabawa sojojin Najeriya bisa jarumtar da suka yi na kai wa 'yan ta'adda hari bayan harin da suka kai a Damboa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel