Rikicin APC: Gwamnoni sun bakaci NEC ta maye gurbin Oshiomhole

Rikicin APC: Gwamnoni sun bakaci NEC ta maye gurbin Oshiomhole

- Gwamnonin jam'iyyar APC suna gaggawan kawar da Oshiomhole daga kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa

- Tuni gwamnonin sun umurci kwamitin zartarwa na jam'iyyar ta maye gurbin tsohon gwamnan na jihar Edo nan ta ke

- Galibi dama gwamnoni su na daga cikin masu fada a ji a ko wane jam'iyya siyasa a Najeriya

Akwai yiwuwar nesa ta zo kusa ga Kwamared Adams Oshiomhole a matayinsa na shugaban jam'iyyar APC na kasa bayan da gwamnonin jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) suka bukaci Kwamitin zartarwa na kasa na jam'iyyar ta maye gurbin sa nan take biyo bayan dakatar da shi da kotu ta yi.

Gwamnonin ta bakin Direkta Janar na Kungiyar Gwamnonin na APC, Salihu Lukman a ranar Juma'a 6 ga watan Maris sun bukaci Oshiomhole ya yi murabus daga mukaminsa.

Magoya bayan gwamna Godwin Obaseki daga jam'iyyar ta APC reshen jihar Edo sun shiga sun fita har sai da aka dakatar da Oshiomhole daga mazabarsa ta karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar.

Wata babban kotun tarayya a Abuja a ranar Laraba ta jadadda hukuncin da jiga-jigan jam'iyyar na APC reshen jihar Edo suka yi na dakatar da Oshiomhole.

Rikicin APC: Gwamnoni sun bakaci NEC ta maye gurbin Oshiomhole
Rikicin APC: Gwamnoni sun bakaci NEC ta maye gurbin Oshiomhole
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu bayan sun sha maganin kara armashin jima'i sun kwana suna zina

Shugabanin na APC sun ki amincew da yunkurin da Oshiomhole ya yi na neman wata kotun tarayya a jihar Kano ta sake dakatarwar da aka yi masa.

Gwamnonin sun ce kafin lokacin da za a warware rikicin jam'iyyar, sun ce ya kamata ayi amfani da sashi na 17 na kundin tsarin jam'iyyar da ya ce ba zai yi wu a bar wata kujera babu wanda zai yi rikon kwarya ba idan an dakatar da mai ita.

Kafin yanzu, akwai jita-jitar cewa Sanata Abiola Ajimobi zai maye gurbing Oshiomhole kafin a warware rikicin jam'iyyar.

A ranar 4 ga watan Maris ne aka sanar da cewa Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo shine mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa.

Sai dai gwamnonin jam'iyyar ba su yi na'am da nadin Ajimobi ba wanda hakan na nufin shugabanin jam'iyyar na jihohi ke jagorancin ragamar jam'iyyar.

A halin yanzu dai 'yan sanda sun mamaye harabar sakatariyar jam'iyyar na kasa sun hana shige da fice.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel