Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano

Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano

Wani abin bakin ciki ya faru a ranar Alhamis yayin da wani yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Rjiyar Lemo, Dan Rimi a jihar Kano.

An tabbatar da mutuwarsa bayan an ciro shi daga cikin ruwan kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara na jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano

Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano
Source: UGC

DUBA WANNAN: Masoya biyu sun mutu bayan sun sha maganin kara armashin jima'i sun kwana suna zina

Ya ce, "Wani Malam Mujittafa Tasiu ne ya kira mu misalin karfe 11.38 na safiyar yana neman dauki kan afkuwar lamarin.

"Bayan samun bayanin, mun yi gaggawar tura tawagar ceton mu zuwa wurin da abin ya faru kuma sun isa misalin karfe 11.52 na safe.

"Ko da isarsu an tarar cewa Muhammad ya rasu kuma an mika gawarsa ga mai unguwar Danrimi Alhaji Yunusa Yahaya."

A wani rahoton, mun kawo muku cewa tsohon dan majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani ya roki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a kan ya yafe wa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a kan duk wani abinda ya yi ba dai-dai ba.

Sani ya sanar da hakan ne a yau Juma’a a wallafa da yayi a shafinsa na Twitter.

Ya yi kira ga Gwamna Ganduje a kan “ya yi yafiya, ya kuma manta da abinda ya wuce ya kyale sarki Sanusi II”. Ya kara da kira ga gwamnan da ya sani cewa mulki na juyi ne kuma watarana zai iya bukatar taimakon Sarkin.

Sarkin Kano din dai na fuskantar sabuwar tuhuma ne daga hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano, a kan zargin damfarar naira biliyan 2.2 na fili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel