Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor

Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor

- A wajen Chinedu Okafor, talla dai ta zama wani abu da ya kawo sauyi a rayuwar shi

- Dan Najeriyan da ya koma jihar Legas din a 2016 ya fara talla ne a cunkoson kan titin jihar

- Okorafor ya fara da tallar gala ne amma daga baya sai ya kara da biskit tare da ruwan lemu

Wani dan Najeriya mai suna Chinedu Okorafor ya bayyana yadda talla a titi ta sauya mishi rayuwar shi gaba daya. Yana samun a kalla naira miliyan daya a kowanne wata daga wannan sana’ar ta shi.

Okorafor, wanda ya koma yankin gabas din kasar nan ta jihar Legas a 2016 da naira dubu daya, riguna biyu da wanduna biyu, ya fada sanar’ar talla a cunkoson titin jihar.

Kamar yadda ya bayyana, kafin ya fara samun kudin da suka kai naira miliyan daya daga wannan sana’ar, ya ziyarci kauyensu kuma mutane na ta sha’awar rayuwar shi ta Legas.

Legit.ng ta gano cewa, dan kasuwar ya dauka matasa 12 aiki wadanda ya taho dasu daga kauyensu don taimaka mishi wajen talla a titin. Okorafor ya fara basu kayan da suka hada da gala da kuma lemukan inda yake basu kashe 30 na ribar da suka samu a ranar.

Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor
Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor
Asali: Original

KU KARANTA: Namiji daya ba zai isheni ba, maza 3 zan aura - Jaruma Ifu Ennada

Joseph ya ce: “A yayin cika musu burikansu na samun abun kashewa, yana biya musu kudin haya tare da hada musu cin abincin dare akai-akai.”

Kamar yadda Joseph ya sanar, Chinedu bai daina hawa kan titin ba ko bayan da yake ba samarin kayan na siyarwa. Sau da yawa yana zuwa tallar tare da su ne.

A karshen 2018, wanda ya cika shekaru biyu cif da zuwan shi jihar Legas, yana da a kalla matasa 100 da ke siyar mishi da kayayyaki a kan titunan jihar. Akwai kuma masu sarin da ke siya daga wajen shi.

Daga nan ne ya kara buda kasuwancin shi inda ya koma siyar da biskit, ruwan lemu da kuma dankali soyayye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel