An dakatar da dan majalisar jihar Jigawa saboda 'kai wa tawagar gwamna hari'

An dakatar da dan majalisar jihar Jigawa saboda 'kai wa tawagar gwamna hari'

Majalisar jihar Jigawa a ranar Juma'a ta dakatar da mamba mai wakiltan mazabar Gumel, Sani Isiyaku dan jami'iyyar APC a kan zarginsa da amfani da 'yan daba.

Ana zarginsa ne da hada baki da wasu 'yan daba da suka kai wa tawagar gwamnan jihar hari.

Premium Times ta yi kokarin ji ta bakin dan majalisar ta wayar tarho amma hakan bai yi wu ba domin lambarsa ba ta shiga a lokacin hada rahoton.

Kakakin majalisar jihar, Idris Garba ne ya sanar da dakatar da shi a zaman majalisar na ranar Alhamis. Ya ce dukkan 'yan majalisar sun amince da matakin dakatar da shi.

An dakatar da dan majalisar jihar Jigawa saboda 'kai wa tawagar gwamna hari'
An dakatar da dan majalisar jihar Jigawa saboda 'kai wa tawagar gwamna hari'
Asali: Twitter

Kakakin majalisar ya ce dan majalisar da aka dakatar ya hada baki da wasu 'yan siyada da 'yan bangan siyasa domin inda suka 'dauke hankalin' tawagar gwamna Muhammad Badaru yayin da suke karamar hukumar Hadejia.

DUBA WANNAN: An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

Kakakin majalisar ya yi ikirarin cewa abinda dan majalisar ya aikata ya saba wa dokokin majalisar jihar 'da na jihar da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya".

Kakakin ya ce, "An dakatar da Mista Isiyaku ne saboda rawar da ya taka a wani rashin da'a da aka aikata duk da cewa shi dan majalisa ne.

"Ana bukatar ya mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa kuma an dakatar da shi daga shugabancin duk wata kwamiti a majalisa daga yau."

Majalisar ta kuma kafa kwamitin bincike na musamman da za ta duba yada aka kashe kudade a majalisar yayin da Sani Isiyaku ya ke shugaban masu rinjaye a majalisar.

A bangarensa, wani dan siyasa, Umar Danjani ya soki matakin da aka dauka na dakatar da dan majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel