Jerin ayyuka 35 da Buhari zai yi da bashin $22.7bn da zai karbo

Jerin ayyuka 35 da Buhari zai yi da bashin $22.7bn da zai karbo

A ranar Alhamis, 5 ga watan Febrairu 2020, Majalisar dattawan tarayya ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari daman karbo bashin $23bn (dala bilyan 22,798,446,773).

A yanzu haka, ana bin Najeriya bashin N26.215 trillion.

Ga yadda gwamnatin Buhari ta shirya kashe kudin bashin da zata karbi da kuma inda ayyukan da za a gudanar suke:

AYYUKAN GINE-GINE

1. Gyaran hanyoyi na gaggawa a fadin tarayya ($434.7m)

2. Bincike kan ginin titi tsakanin Legas da Abidjan, kasar Koddibuwa ($1.5m)

3. Jirgin kasan birnin tarayya Abuja (Sashe na biyu $1.25bn; )

4. Titin East-west road ($800m; Niger Delta)

5. Shirin gine-ginen gidaje a fadin tarayya ($100m)

6. Ginin layin dogo da Jirgin kasan Ibadan zuwa Kano ($5.53bn)

7. Ginin layin dogo da Jirgin kasan Calabar zuwa Fatakwal zuwa Onne ($3.47bn; Cross River da Rivers )

AYYUKAN WALWALA DA JIN DADIN ALUMMA

8. Aikin taimakon alummar kasa ($500m)

9. Shirin farfado da rayuwar mutane bayan rikice-rikice ($200m, Arewa maso gabas)

10. Aikin raya ilimi, kiwon lafiya, walwala da jin kai na yankin Arewa maso gabas ($100m;)

WUTAN LANTARKI

11. Aikin tura wutan lantarki ($200m; Lagos, Ogun)

12. Shirin horon matasa a bangaren wutan lantarki ($50m; FCT, Lagos, Ogun. Kano, Plateau, Niger, Enugu, Kaduna da Cross River)

13. Shirin inganta kayayyakin sufurin kamfanin tura wutar lantarkin Najerya ($200m)

14. Aikin samar da wutan lantarkin Mambila ($4.8bn; Taraba)

15. Sabon shirin tura lantarki ($364m)

ILIMI

16. Shirin samar da ingataccen ilimi ga kowa BESDA ($500m, fadin tarayya)

TATTALIN ARZIKI

17. Aikin cigaban maaikatar kudi ($520m)

18. Shirin sauya tattalin arzikin jihar Kaduna ($35m, Kaduna)

19. Aikin cigaban maaikatar wuta ($450m, min. of power)

20. Ayyukan cigaban kananan yan kasuwa ($1.28bn; nationwide)

SADARWA

21. Zamananta gidan talabijin NTA zuwa ($500m)

22. Shirin cigaban ilimin sadarwa da fasahar zaman, sashe na biyu ($328.1m; Lagos, Abuja, Ibadan, Akure, Maiduguri, Lokoja, Kaduna, Akwanga, Bauchi, Kano, Katsina)

AIKIN NOMA

23. Aikin masana'antar sarrafa kayan abinci a jihar Kogi ($100m, Kogi)

24. Aikin cigaban sashen aikin noma (ATASP) ($200m)

25.Aikin masana'antun sarrafa kayan abinci a fadin tarayya (500m)

KIWON LAFIYA DA RUWAN SHA

26. Aikin lura da cututtuka a fadin Afrika ta yamma ($90m)

27. Aikin kiwon lafiya na jihar Katsina ($110m, Katsina)

28. Aikin samar da ruwan sha a Arewa maso gabas da jihar Plateau ($150m)

29. Aikin samar da ruwan sha a Abuja ($381m; FCT)

SHUGABANCI

30. Aikin inganta harkar kudi a ma'aikatun gwamnati ($200m)

31. Karfafa ma'aikatar ayyuka da gidaje ($33.7m)

YANAYI DA MAADINAI

32. Hukumar tafkin Chadi ($13m, kasa da kasa)

33. Aikin cigaba da sabawa da sauyin yanayi a yankin Nijar ($6m; Nigeria da Niger)

34. Cigaban kamfanonin hako ma'adinai a fadin tarayya ($150m)

Asali: Legit.ng

Online view pixel