Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Togo

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Togo

Kasar Togo, kasa a yammacin Afrika ta tabbatar da bullar sabuwar cutar Coronavirus a kasar sanadiyar wata yar kasar da ta ziyarci kasashen Turai uku a makonni 5 da suka da suka gabata.

Gwamnatin kasar Togo ta sanar da hakan ranar Juma'a. 6 ga Maris, 2020 a Lome, babbar birnin kasar.

An bayyana cewa matar, yar shekara 42 da haihuwa ta ziyarci kasar Benin, Jamus, Faransa da Turkiyya a cikin watan Febrairu da Maris.

An killaceta yanzu kuma ana kula da ita.

Mun kawo muku rahoton cewa kasar Kamaru ta tabbatar da bullar sabuwar cutar Coronavirus a kasar sanadiyar wani dan kasan Faransa da ya shiga Yaounde, babbar birnin kasar ranar 24 ga Febrairu, gwamnatin ta sanar ranar Juma'a.

Tuni an killace Baturen, dan shekara 58 a asibiti, ma'aikatar kiwon lafiyan kasar suka sanar.

Kasashen Afrikan da cutar ta bulla kawo yanzu sune Misra, Algeria, Najeriya, Afrika ta kudu, Kamaru, Senegal da Togo.

A lissafin yau Juma'a, mutane 100,330 suka kamu da cutar a fadin duniya, mutane 3,408 sun mutu, kuma mutane 55,694 sun samu warkewa daga cutar.

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Togo
Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Togo
Asali: Twitter

A bangare guda, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Coronavirus Najeriya ya murmure kuma za'a sallameshi daga inda aka killaceshi nan ba da dadewa ba.

Sakataren yada labaran gwamnan, Kunle Somorin, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kamfanin Simintin, Lafarge PLC, karkashin jagorancin shugabanta, Khaleed El Dokani, a ofishinsa dake Oke-Mosan, Abekuta.

Yace: "Mara lafiyan yana cikin halin lafiya kuma za'a sallameshi nan ba da dadewa ba."

Gwamnan ya bayyana cewa cutar babbar kalubale ce ga jihar Ogun, a matsayinta na jihar manyan masana'antun Najeriya.

Ya lashi takobin cewa gwamnatinsa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen takaita yaduwar cutar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel