An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

Auren masoyan Instagram da za a yi a watan Maris din nan tsakanin Sulaiman dan Panshekara da ke Kano da kuma Jeanine Sanchez an dage shi har sai baba ta gani. An dage auren Sulaiman Panshekara da masoyiyarsa Jeanine Sanchez mai shekaru 46 ne saboda hatimin shiga Amurka da aka haramtawa ‘yan Najeriya.

Da farko dai, an saka ranar auren Sulaiman Panshekara da baturiyar kasar Amurka da ta biyosa har Najeriya. Amma kuma an dage auren ne sakamakon haramtawa ‘yan Najeriya visa da aka yi ta shiga kasar Amurka. Baturiyar budurwar Sulaiman kuma amarya Jeanine, za ta nemi wasu halastattun hanyoyin mayar da angonta kasar Amurkan kafin a daura auren.

A yayin tattaunawa ta wayar tafi da gidanka tsakanin jaridar Daily Trust da mahaifin ango Sulaiman, yace za a sanar da sabuwar ranar auren ne bayan Sanchez ta samo wasu hanyoyin samuwar takardar komawar dan sa Amurka.

Sulaiman mai shekaru 26 da Sanchez mahaifiyar yara biyu, sun fara soyayya ne a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram kusan shekara daya da ta gabata. Ta ziyarcesa a Panshekara a watan Janairu kuma ta bukaci aurensa tare da tafiya da shi kasar Amurka.

An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka

An dage auren Suleiman Panshekara da masoyiyarsa 'yar Amurka
Source: UGC

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje

Isa yana aji biyu ne a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano. Tuni kuwa ya nuna amincewarsa na tafiya kasar Amurka don kammala karatunsa tare da gina soyayyar aure da masoyiyarsa baturiyar Amurka.

Kamar yadda mahaifin angon yace, “Ba za a yi auren a watan Maris ba kamar yadda aka tsara da farko, saboda sabbin tsare-tsaren gwamnatin kasar Amurka na hana ‘yan Najeriya hatimin shiga kasar. Amma kuma matar na iya bakin kokarinta wajen samo hanyar samuwar takardun zaman Sulaiman a matsayin dan kasar. Bayan ta kammala kuwa za a saka sabuwar ranar biki.”

Idan za a tuna, mahaifin angon ya tuntubi hukumar tsaro ta faraen kaya don hada kai da abokanta na CIA da FBI don karfafa bincike a kan sirikarsa. A yayin da aka tambayi dan sandan mai murabus, ya ce ana ci gaba da bincike har yanzu.

Ya ce iyalansa sun kosa lokacin da burin Sulaiman zai cika na auren rabin ransa baturiyar kasar Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel