Da duminsa: Coronavirus ta bulla a kasar Kamaru

Da duminsa: Coronavirus ta bulla a kasar Kamaru

Kasar Kamaru ta tabbatar da bullar sabuwar cutar Coronavirus a kasar sanadiyar wani dan kasan Faransa da ya shiga Yaounde, babbar birnin kasar ranar 24 ga Febrairu, gwamnatin ta sanar ranar Juma'a.

Tuni an killace Baturen, dan shekara 58 a asibiti, ma'aikatar kiwon lafiyan kasar suka sanar.

Mun kawo muku a baya cewa Kasar Tunisiya da kasar Senegal sun tabbatar da bullar cutar Coronavirus na farko, hakan ya ya kai adadin kasashen da ta bulla a nahiyar Afrika biyar.

Gabanin shigarta kasashen nan biyu a yau Litinin, kasashen Misra, Algeria, da Najeriya sun tabbatar da bullar cutar da ta hallaka akalla mutane 3000 a fadin duniya.

A wani hira da manema labarai da ministan kiwon lafiyan kasar Senegal, ya shirya a birnin Dakar ranar Litinin, ya bayyana cewa wani dan kasan Faransa ya shigo da cutar kasar.

A kasar Tunisiya kuwa, wani dan kasar Italiya ne ya jajubo musu cutar.

Da duminsa: Coronavirus ta bulla a kasar Kamaru

Da duminsa: Coronavirus ta bulla a kasar Kamaru
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel