Yanzu-yanzu: Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi

Yanzu-yanzu: Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Coronavirus Najeriya ya murmure kuma za'a sallameshi daga inda aka killaceshi nan ba da dadewa ba.

Sakataren yada labaran gwamnan, Kunle Somorin, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kamfanin Simintin, Lafarge PLC, karkashin jagorancin shugabanta, Khaleed El Dokani, a ofishinsa dake Oke-Mosan, Abekuta.

Yace: "Mara lafiyan yana cikin halin lafiya kuma za'a sallameshi nan ba da dadewa ba."

Gwamnan ya bayyana cewa cutar babbar kalubale ce ga jihar Ogun, a matsayinta na jihar manyan masana'antun Najeriya.

Ya lashi takobin cewa gwamnatinsa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen takaita yaduwar cutar ba.

Yanzu-yanzu: Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi

Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi
Source: Twitter

Mutan duniya gaba daya a halin yanzu na gujewa wuraren da akwai taron jama'a, da dama sun soke tafiye-tafiye, yayinda wasu suka koma zaman gida gaba baya gudun kamuwa da cutar Coronavirus da ta addabi duniya.

Kawo yanzu, akalla mutane 90,000 sun kamu da cutar kuma 3000 sun rigamu gidan gaskiya kuma ta ratsa akalla kasashe 66 a fadin duniya.

Kasashen irinsu Saudiyya, Iran, Kuwait, Qatar da sauran manyan kasashen Musulmai sun kafa sabbin dokokin takaita cutar kuma hakan yana shafan rayuwan Musulmai.

Kungiyar kiwon Lafiya ta duniya WHO ta shawarci jama’a da su rinka amfani da naurorin zamani wajen bukatunsu na kudi, domin kudi kan iya jawo yaduwar coronavirus.

Cutar Coronavirus zata iya zama akan kudi na tsawon kwanaki, Kungiyar kiwon lafiya tayi gargadi a daren Litinin.

Cutar Coronavirus zata iya yaduwa ta hanyar abubuwan da suke dauke da cutar da kuma haduwa da wadanda suke dauke da cutar, cewar kungiyar WHO.

"Domin hana yaduwar cutar, mutane su rinka amfani da naurorin zamani domin gudanar da bukatunsu na kudi bayan haka kuma su wanke hannayensu bayan sun taba kudin" cewar mai Magana da yawun kungiyar WHO.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel