Kisan Budurwa bayan ta karbi Musulunci ya tayar da hankali a Kaduna

Kisan Budurwa bayan ta karbi Musulunci ya tayar da hankali a Kaduna

An yiwa wata Budurwa, Aisha Aliyu, kisan gilla a cikin dakinta kwanaki bayan ta karbi addinin Musulunci a Unguwan Mangu, Saminaka, karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Kisan Aisha, yar shekara 31 da haihuwa ya tayar da kura a ranar Lahadin da ya gabata ya tayar da hukumar a garin na Samimaka. Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa an cakawa Alisha Aliyu wuka sau hudu a wuya har lahira kuma aka tsinci gawarta cikin daki

An tattaro cewa sai da malaman addini, jami’an tsaro da shugabannin unguwa suka sanya baki kafin aka kwantar da kuran.

Dan’uwan maragayiyar, Bulus Aliyu, yayinda yake bada abinda ya faru ya bayyana cewa an tsinci gawar ‘yar uwarsa ne cikin jinni da safiyar Litinin.

Yace: “Mun samu labarin cewa an caka mata wuka a wuya sau hudu, sai muka dauki gawarta kuma muka birne.”

KU KARANTA: Lakcarorin jami’an da suka ku yin rijista a manhajar IPPIS ba zasu samu albashin Febrairu ba – Ministar Kudi

Bulus ya musanta rahoton zargin da ake yi cewa ya uwanta ne suka hada baki suka kasheta saboda ta karbi Musulunci, ya ce “Muna da Musulmai a danginmu, babbar yayarmu Musulma ce kuma bamu taba tsangwamarta ba saboda zabinta ne.”

Yayar marigayiyar, Jamila Aliyu, ta ce kanwarta ta karbi shahada ne kimanin shekara daya yanzu a wajenta, tace “ta zo wajena lokacin da nike Kano kuma tace min tana son Musulunta.”

Yayind aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda, ASP Muhammad Jalinge, y ace kisanta ba da alaka da kowarta Musulunci kuma bincike ya nuna cewa an sace wayoyinta biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel