Coronavirus: Masarautar Saudiyya ta bude Masallatan Makkah da Madina bayan tsaftace su

Coronavirus: Masarautar Saudiyya ta bude Masallatan Makkah da Madina bayan tsaftace su

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bude masallatan Makkah da Madina da sanyin safiyar Juma’a bayan ta garkamesu a daren Alhamis domin tsaftacesu daga yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus.

An bude masallatan ne domin bayar da damar gudanar da Sallar Juma’a ga al’ummar Musulmai, amma za’a cigaba da rufe harabar Ka’abah da kuma tazarar dake tsakanin dutsen Safa da Marwa, duk a kokarin dakatar da yaduwar cutar.

KU KARANTA: Oshiomole ya bayyana babban dalilin da yasa makiyansa ke kokarin cire daga shugabantar APC

Gwamnatin ta bayyana cewa a iya cikin masallaci kadai za’a bari masallata su gudanar da sallah.

Zuwa yanzu an samu mutane biyar da suka kamu da cutar Coronavirus, kuma dukkaninsu sun shigo ne ta kasashen Bahrain da Kuwait, amma daga kasar Iran suka taso gaba dayansu, don haka gwamnatin Saudiyya ta haramta ma yan kasarta zuwa kasar Iran, tare da kudurin hukunta duk wanda ya karya wannan umarni.

A ranar Laraba ne gwamnatin Saudiyya ta dakatar da yan kasarta da mazauna garin Makkah daga gudanar da aikin Umrah domin kiyaye yaduwar cutar Coronavirus, ga wasu sauye sauye guda bakwai da gwamnatin Saudiyya ta samar don kare yaduwar cutar;

- Za’a kulle Masallatan Makkah da Madina bayan sallar Isha, a budesu kafin sallar Asubah

- Za’a kulle Farfajiyar Ka’abah da tazarar dake tsakanin Safa da Marwa har sai yadda hali yayi

- An kyale jama’an garin Makkah su shiga Masallacin Harami

- An hana kowa Umrah

- An hana ci da sha a cikin harami

- Za’a kulle famfon ruwan Zamzam

- Za’a kulle Baqiyyah da Rawdah da zarar an isar da Sallah.

A wani labarin kuma, kungiyar kananan likitoci a jahar Kaduna, watau Association of Resident Doctors, ta fara yajin aikin sai baba ta ji daga ranar Laraba, 4 ga watan Maris sakamakon zargin gwamnatin jahar da suka yi da rashin cika alkawari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel