Boko Haram na cigaba da fuskantar ruwan bama bamai daga jiragen yakin Najeriya

Boko Haram na cigaba da fuskantar ruwan bama bamai daga jiragen yakin Najeriya

Bangaren dakarun rundunar Sojan sama na Operation Lafiya Dole sun cigaba da yi ma mayakan kungiyar yan ta’addan kungiyar Boko Haram ruwan wuta da bama bamai a yankin Bakari Gana dake gefen dajin Sambisa.

Daily Trust ta ruwaito daraktan watsa labaru na rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris, inda ya ce sun kai hare haren ne a ranar Laraba a jahar Borno.

KU KARANTA: Oshiomole ya bayyana babban dalilin da yasa makiyansa ke kokarin cire daga shugabantar APC

Daramola ya bayyana cewa sun kai harin ne don kaddamar da wani sabon operation mai taken “Operatio Decisive Edge” da mahukunta a rundunar Sojan sama suka kirkiro shi don tabbatar da gamawa da Boko Haram.

Daramola ya kara da cewa an kirkiri Operation Decisive Edge ne don lalubo duk inda mafakar ko mabuyar yan Boko Haram take tare da ragargazarsa, musamman inda Sojoji ba za su iya shigar a kafa ba saboda yanayin lungun ko kuma sun zagaye shi da bamabaman da suka binne.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sojan saman ya bayyana cewa sun kai hare haren ne bayan tattara bayanan sirri ta hanyar amfani da na’urorin zamani wanda suka tabbatar da yan ta’adda suna ajiye man fetir da sauran kayan aiki a wasu bukkoki dake Bakari Gana.

“Jim kadan bayan tabbatar da mafakar, muka tura jiragen yakinmu wanda suka kaddamar da hare haren da suka tarwatsa bukkokin duka, har muka hangi tankokin ajiyan man sun kama da wuta, haka zalika wasu yan ta’adda tsare sansanin sun mutu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu dakarun Sojojin Najeriya dake yaki da kungiyar Boko Haram a jahar Borno sun aika ma sakon koke ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai game da wani babban Soja dake cinye hakkokinsu.

Sojojin sun bayyana cewa babban Sojan yana cinye hakkokinsu da alawus alawus, kuma ya ki biyansu sabon alawus N200 na kudin sigari da rundunar Sojan kasa ta fara biya tun a watan Janairu.

Sojojin sun ce a maimakon alawus din kudin walwala na N24,000, wanda ya hada da N12,000 da babban hafsan Soja yake biyansu, amma sai kwamandan nasu yake biyansu N12,000 kacal, amma sauran kwamandojin bataliya suna biyan Sojojin bataliyars N24,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel