Za a fara biyan 'yan N-Power allawus din Janairu da Fabrairu ranar Juma'a - FG

Za a fara biyan 'yan N-Power allawus din Janairu da Fabrairu ranar Juma'a - FG

- Gwamnatin tarayya ta bada sanarwa a kan tsaikon da aka samu wajen biyan masu aikin N-Power

- Wani ahdimin shugaban kasa mai suna Afolabi Imoukhuede, yace za a fara biyan masu aikin N-Power din ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Maris

- Imoukhuede ya jaddada cewa albashin masu digiri na watan Fabrairun nan da ta gabata na daban ne

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa masu aikin N-Power zasu fara samun albashinsu na watan janairu da Fabrairu a ranar Juma’a, 6 ga watan Maris.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa babban mai bayar da shawar ga shugaban kasa a kan samar da ayyuka da habaka matasa, Afolavi Imoukhuede, ya ce gwamnatin tarayyar ta shawo kan dukkan abubuwan da ke bata matsala a kan N-Power din.

Legit.ng ta gano cewa gwamnatin tarayyar za ta saki kudin wadanda ba masu digiri ba da kuma masu digirin na watan Fabrairu a ranar Juma’a 6 ga watan Maris.

Za a fara biyan 'yan N-Power allawus din Janairu da Fabrairu ranar Juma'a - FG

Za a fara biyan 'yan N-Power allawus din Janairu da Fabrairu ranar Juma'a - FG
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Imoukhued ya sanar da manema labarai a ranar Alhamis agarin Abuja cewa ana ta kokarin biyan ma’aikatan ne bayan korafinsu da hukumar ke fsukanta na rashin biyansu albashi tun bayan da aka sauya wa cibiyar ma’aikata.

Hakazalika, Kamfanin Dilllancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a yayin rokon masu aikin a kan tsaikon da aka samu, Imoukhuede y ace rashin biyan da aka samu na watanni an yi shine saboda son fahimtar cibiyar da kyau bayan sauya mata ma’aikata da aka yi.

“Ministar ta ce tana bukatar fahimtar yanayin cibiyar wanda kuma duk mun mayar da hankali wajen yin hakan. Ina da tabbacin cewa sabuwar ma’aikatar ta kammala komai kuma mun fi karfin komai a yanzu. Na san da kudin watan janairu duk da bai zo da wuri, amma za a biya” y ace.

“Na san da cewa ba a biya marasa digiri ba amma a halin yanzu, an kai karshen matsalarsu kuma za a biya su kafin ko ranar Juma’a na wannan makon nan,” Imoukhuede yace.

Yace albashin masu digiri na watan Fabrairu ya dau mataki na gaban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel