Sarki Sanusi a bukaci masu bincikensa sun sanya masa wani rana domin ya masa sammacinsu

Sarki Sanusi a bukaci masu bincikensa sun sanya masa wani rana domin ya masa sammacinsu

Shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimingado, ya tabbatar da labarin cewa hukumar ta sammaci mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusui na biyu, kan zargin badakalar N2.2bn na filaye.

Amma ya bayyana cewa masarautar ta bukaci hukumar ta sanya wani rana daban domin sarkin ya bayyana.

Rimingado ya ce hukumar za ta zabi wani rana domin sarkin ya gurfana.

"Zan yiwa manema labarai bayani a yau kuma hukumar zata sanar da matsayarta kan lamarin nan." Ya ce.

A wani labarin mai alaka, Majalisar dokokin jahar Kano ta bude sabon shafin binciken Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, kan wasu korafe-korafe da wasu mazauna jahar suka gabatar a gabanta, inda suke zarginsa da ci wa al’adun garin fuska.

Shugaban kwamitin jahar kan kananan hukumomi da masarautu, Zubairu Hamza-Masu ya bayyana a zauren majalisar cewa kwamitin ya karbi korafe-korafe biyu, daya daga wani Muhammad Muktar, sannan na biyun daga Shugaban hukumar KSPCE, Muhammad Bello-Abdullahi.

Dukkaninsu su biyun suna zargin Sarkin da wofantar da al’adun iyaye da kakanni na jahar da kuma rashin martaba masarautar.

Hamza ya ce dukkanin masu korafin na neman majalisar da ya zurfafa bincike kan zargin da suka gabatar mata.

Shugaban majalisar dokokin, Abdulaziz Gafasa ya mika korafin ga kwamitin majalisar ta yi bincike cikin mako guda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel