Hanyoyi 5 da cutar Coronavirus ta sauya rayuwar Musulman duniya
Mutan duniya gaba daya a halin yanzu na gujewa wuraren da akwai taron jama'a, da dama na fasa tafiye-tafiye, yayinda wasu suka koma zaman gida gaba baya gudun kamuwa da cutar Coronavirus da ta addabi duniya.
Kawo yanzu, akalla mutane 90,000 sun kamu da cutar kuma 3000 sun rigamu gidan gaskiya kuma ta ratsa akalla kasashe 66 a fadin duniya.
Kasashen irinsu Saudiyya, Iran, Kuwait, Qatar da sauran manyan kasashen Musulmai sun kafa sabbin dokokin takaita cutar kuma hakan yana shafan rayuwan Musulmai.
Ga hanyoyi biyar da cutar Coronavirus ta sauya rayuwar Musulmai duniya:
1. Dakatad da aikin Umrah
Gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah da ziyarar Masallacin Annabi mai girma ga dukkan yan kasar da mazauna sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar.
A yau kuwa, Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin babban limami, Sheikh Abdur-Rahman As-Sudais ta kaddamar da feshi da tsaftace Mataaf na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona.

Asali: Facebook
2. Kasar Iran ta dakatad da Sallar Juma'a a manyan biranenta
Kasar Iran na daya daga cikin kasashen da ke fama da yaduwar cutar inda karuwa abin yake kulli yaumin. Kawo zuwa ranar Laraba, mutane 2,992 sun kamu da cutar kuma 92 sun mutu.
3. An hana mutane Musafaha
Shugaban al'ummar Musulmai a kasar Singapore ya shawarci al'ummarsa sun kiyayi musafaha a wannan lokaci saboda ana iya daukan cutar ta haka.
A cewar Jaridar The Straits Times, Ministan harkokin addinin Musuluncin kasar, Masagos Zulkifil, ya yi kira da al'ummarsa su daina musafaha
4. Kowa ya zo da Sallayarsa Masallaci
Bugu da kari, Ministan harkokin addinin Musuluncin kasar, Masagos Zulkifil, ya shawarci Musulman kasar su rika zuwa da taburma ko daddumarsu Masallaci kuam su daina Sallah a na wani.
Hakazalika masallata da dama na tsoron hada kafa da juna cikin sahu kuma hakan na daga cikin wajabcin Sallar jam'i.
5. Kowa ya rika Sallah a gidansa
Duk da cewar cutar bata shiga kasar Tajikistan ba tukun, gwamnatin kasar mai yawan mabiyan addinin Islama milyan tara ta yi kira da al'ummar su rika Sallarsu a gida.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng