Magidanci ya kashe kansa bayan sun samu saɓani da matarsa

Magidanci ya kashe kansa bayan sun samu saɓani da matarsa

- Wani mutum a jihar Anambra ya kashe kansa sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakaninsa da matarsa

- Mutumin mai suna Samuel Nweke ya sagale kansa ne a kan fadan da suka yi da matarsa kuma ya bar wasiyya rubutacciya

- Bayan rahoton ne aka tura jami’an ‘yan sandan don ziyarar wajen da abun ya faru. Sun dauko hotunan gawar bayan likita ya tabbatar da cewa ya mutu

Wani mutum a jihar Anambra ya kashe kansa sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakaninsa da matarsa.

Mutumin mai suna Samuel Nweke ya sagale kansa ne a kan fadan da suka yi da matarsa kuma ya bar wasiyya rubutacciya.

Kamar yadda takardar da Haruna Muhammad, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda jihar Anambra, wacce ya ba manema labarai a garin Awka, yace fadan da mamacin yayi da matar shi ne yasa ta bar shi ta gudu. Hakan kuwa yasa ya kashe kan shi.

Magidanci ya kashe kansa bayan sun samu saɓani da matarsa

Magidanci ya kashe kansa bayan sun samu saɓani da matarsa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: IGP ya bayyana su waye 'yan bindigan yankin Arewa maso Yamma

“A ranar 4 ga watan Maris din 2020 ne wajen karfe 12:10 na rana aka kai rahoton ganin gawar Samule Nweke mai shekaru 47 a duniya. An ga gawar shi ne a daki na biyar da ke titin Chief Nwankwo da ke Awada a karamar hukumar Idemili na jihar Anambra. " takardar ta ce.

“Bayan rahoton ne aka tura jami’an ‘yan sandan don ziyarar wajen da abun ya faru. Sun dauko hotunan gawar bayan likita ya tabbatar da cewa ya mutu. Babu alamun fada ko tashin hankali da aka gani a tare da gawar amma sai aka ga wasiyya a kusa da gawar,” ta kara da cewa.

Amma kuma a halin yanzu, Haruna ya ce an fara binciken farko wanda ya bayyana cewa magidancin yayi fada da matarsa ne inda ta bar mishi gidan a ranar 25 ga watan Fabrairun 2020.

Ana zargin cewa abinda matar shi din tayi ne ya bata masa rai har ya kashe kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel