Mutumin da ya nemi aiki sau 200 bai samu ba yanzu yana samun sama da naira miliyan hudu duk wata

Mutumin da ya nemi aiki sau 200 bai samu ba yanzu yana samun sama da naira miliyan hudu duk wata

- Amos Nyambane ya kammala digirinsa a shekarar 2017 daga jami’ar Dedan Kimathi

- Ya nemi ayyuka a kalla sun kai 200 amma bai samu ba har zuwa karshen shekarar 2017 din

- A halin yanzu matashin na samun GHC62,511.63 a duk wata ta sana’ar siyar da ‘ya’yan kaji

A lokacin da Amos Nyambane ya kammala digirin shi a 2017, yana ta tunanin yadda zai samu aikin gwamnati. Bai taba tsammanin cewa ba zai yi nasarar samun aikin ba ko kuma wata sana’ar da zai samu abin duniya ba, har sai bayan ya bata shekaru hudu yana neman aiki.

Tsohon dalibin jami’ar Dedan Kimathi din ya yanke hukuncin fara kiwon kaji da kudin da yake samu daga wajen gini da ya fara. Ya siya kaji 40 kamar yadda yace amma sai aka fara samun matsala. Iyayen shi duk sun damu kuma sun kosa da yadda kiwon ke tafiya.

‘A lokacin da na fara kiwon, mahaifiyata ba ta goyon baya. Sau da yawa muna fada kuma ta kan yi yunkurin korata tare da cewa in nema aikin yi,” yace.

A halin yanzu, ya mallaki kaji masu saka kwai 2,000 kuma suna samar da tsaki 20,000 kowanne wata. Yana samun ribar kusan Ksh miliyan 1.2.

“A kowanne wata ina siyar da tsaki 20,000 ga manoma a fadin kasar nan. Duk tsako mai kwana daya ina siyar da shi a kan KSh 75 da KSh 85, amma ya dogara da irin tsakon ne.” Yace.

Mutumin da ya nemi aiki sau 200 bai samu ba yanzu yana samun sama da naira miliyan hudu duk wata
Mutumin da ya nemi aiki sau 200 bai samu ba yanzu yana samun sama da naira miliyan hudu duk wata
Asali: UGC

DUBA WANNAN: A dinga barin mata suna auren maza biyu ko da za a samu akasi daya ya mutu - Jarumar fim

Bayan siyar da tsaki, yana siyar da kwayaye wadanda basu iya kyankyashe kansu. “Ba dukkan kwai bane suke iya kyankyashewa. Wadandda suka kasa kyankyashewa ina siyar da su a matsayin kwai kuma ta nan wata riba ce daban,” ya kara da cewa.

Hakazalika, duk kajin da suka daina yin kwai ana ciresu a gefe daya inda ake basu abincin da zai sa su girma don siyarwa masu gidan abinci.

Dan kasuwar ya bayyana cewa bayan siya abincin kajin. Yana hadawa ne da kanshi kuma a cikin gida.

Da kudin da yake samu a wannan kiwon ne ya siya ababen hawa har guda hudu. Da wadannan ababen hawan kuwa yake kai kajin da kwan duk inda ya kamata idan ana son siye

Amma kuma babban kalubalen da yake fama da shi shine rashin gaskiyar wadanda ke aiki a karkashin shi har su biyar. Ya ce wannan kalubale ne babba. A duk lokacin da baya nan, a maimakon kwai 2,000 daga kaji 2,000, sai dai ya kare da kwai 1,800.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel