Yan sanda sun bazama neman mawakin da yayi wakar batanci a kan manzon Allah a Kano

Yan sanda sun bazama neman mawakin da yayi wakar batanci a kan manzon Allah a Kano

Jamian hukumar yan sanda a Kano sun bazama neman wani mawaki, Yahaya Sharif Aminu, kan wata wakar batanci da yayi a kan manzon Allah (SAW) wanda ya janyo cece-kuce har aka kaiwa iyayensa hari.

Wasu matasa sun dira ofishin Hisbah a ranar Laraba a kan zargin wata waka da aka yi na cin mutuncin manzon tsira Annabi Muhammad (SAW).

Masu zanga-zangar da ke dauke da takardu masu rubutu sun yi ikirarin cewa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suna jan kafa wurin daukan mataki a kan lamarin.

Jagorar masu zanga-zangan, Idris Ibrahim (da aka fi sani ba Baba Idris) ya ce sun zo ne su sanar da gwamnati ta dauki mataki a kan lamarin idan kuma ba haka ba su za su dauki matakin da kansu.

Mista Ibrahim ya ce a baya an samu afkuwar irin wadannan abubuwan a jihar kuma hukumomin tsaro ba su dauki matakan da ya dace a kai ba.

Wani Yahaya Sharif-Aminu ne ya yi wata waka da ke dauke da wasu kalamai da ake zargin na batanci ne ga Annabi Muhammadu (SAW). Hakan ya yi sanadiyar rushe gidan mawakin kuma ya tsere daga unguwar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja

A ranar Juma'a da ta gabata, wasu fusatattun matasa sun bankawa gidan mawakin wuta a rukunin gidaje na Sharifai da karamar hukumar Kano Municipal a kan wakar.

Wakar, wacce nan da nan ta zagaya gari bayan an wallafa ta a dandalin sada zumunta, ta fusata matasan da suka yi yunkurin kone gidan su mawakin kurmus.

An gano cewa matashin mawakin, Yahaya Sharif Aminu, mabiyin mazhabar 'Faidha' ne a cikin darikar Tijjaniyya.

'Yan 'Faidha' sun yi kaurin suna wajen fifita soyayyar Shaikh Ibrahim Nyass a kan soyayyar annabi Muhammad (SAW) da Allah.

Albarkar mata da kananan yara da ke cikin gidan yasa matasan basu cinna masa wuta ba, kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel