Oshiomhole ya daukaka kara kan dakatar da shi da kotu ta yi

Oshiomhole ya daukaka kara kan dakatar da shi da kotu ta yi

Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya daukaka kara a kan hukuncin babban kotu na dakatar da shi daga kujerarsa na shugaban jam'iyya.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba, wata babban kotu da ke birnin tarayya Abuja ta dakatar da Oshiomhole daga kujerarsa na shugaban jam'iyya.

Ta bayar da umurnin Mista Oshiomhole ya koma gefe har zuwa lokacin da aka yanke hukunci kan karar da aka shigar a kansa a kotu na neman tsige shi baki daya daga mukamin shugaban jam'iyyar.

Oshiomhole ya daukaka kara kan dakatar da shi da kotu ta yi

Oshiomhole ya daukaka kara kan dakatar da shi da kotu ta yi
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Da ya ke magana a sakatariyar jam'iyyar na kasa, sakataren jam'iyyar na wucin gadi, Victor Giadam ya ce APC jam'iyya ce mai biyaya ga doka saboda haka za ta bi umurnin kotu ta dakatar da Oshiomhole.

A takardun da ya gabatar na daukaka karar, Mista Oshiomhole ya soki hukuncin da kotun ta yanke.

Wadanda ya yi karar sun hada da Mista Mustapha Salihu, mataimakin shu6 jam'iyyar na kasa (yankin Arewa maso Gabas) da kuma shugaban jam'iyyar reshen jihar Edo, Anslem Ojezua wanda ke biyaya ga gwamnan jihar Mista Obaseki.

Sauran sun hada Sani Gomna, Oshawo Steven, Fani Wabulari, Princewill Ejogbarado, Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya da kuma Hukumar 'yan sandan farar hula SSS.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel