Sokoto: An kama wata dilaliyar wiwi da aka kwashe shekaru 10 ana neman ta ruwa a jallo

Sokoto: An kama wata dilaliyar wiwi da aka kwashe shekaru 10 ana neman ta ruwa a jallo

Jami'an hukumar yaki da hana fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama wata mata da suka kwashe shekaru 10 suna nema ruwa a jallo a jihar Sokoto.

Wacce ake zargin da aka yi holen ta tare da wasu dilalan miyagun kwayoyi 18 an kama ta ne a ranar 28 ga watan Fabrairu.

An gano cewar an samu allurar pentazocine da ke cikin rukuni na 'A' na haramtattun kwayoyi na duniya a tare da matar da ake zargin da ake ce sunan ta Madam Queen kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Sokoto: An kama wata dilaliyar wiwi da aka kwashe shekaru 10 ana neman ta ruwa a jallo
Sokoto: An kama wata dilaliyar wiwi da aka kwashe shekaru 10 ana neman ta ruwa a jallo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Da ya ke tabbatar da kama matar, Kwamandan NDLEA na Sokoto, Mista Yakubu Kibo ya ce;

"Mun kama wata hatsabibiyar dilaliyar wiwi a jihar mai suna Madam Queen daga kauyen Raymond.

"Mun kwashe kimanin shekaru 10 muna neman Madam Auren kuma a ranar 28 ga watan Fabrairu mun damke ta tare da yaron da ke taya ta sayar da ƙwayar.

"Wannan karon, ba wiwi kadai bane, yanzu tana sayar da kwayoyi daban-daban. Baya ga wiwi, mun kama ta da wasu kwayoyi da suka hada da allurar pentazocine."

Kibo ya ƙara da cewa rundunar ta kwato muggan kwayoyi da nauyin su ya kai kilogram 141.534 a watan Fabrairun 2020. Ƙwayoyin sun hada da wiwi da nauyinsa ya kai 134.138 da kayan maye da tramadol diazepam da allurar pentazocine.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel