Rikicin albashin ma’aikata: Likitoci a jahar Kaduna sun shiga yajin aikin dindindin

Rikicin albashin ma’aikata: Likitoci a jahar Kaduna sun shiga yajin aikin dindindin

Kungiyar kananan likitoci a jahar Kaduna, watau Association of Resident Doctors, ta fara yajin aikin sai baba ta ji daga ranar Laraba, 4 ga watan Maris sakamakon zargin gwamnatin jahar da suka yi da rashin cika alkawari.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban ARD, Emmanuel Joseph ya bayyana haka a garin Kaduna, inda yace sun dauki wannan mataki ne saboda gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na gyara albashin likitocin, tare da magance wasu matsalolin kiwon lafiya a jahar.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Nassarawa za ta kwashe almajirai 63,000 zuwa jahohinsu na asali

“Don haka muka yanke hukuncin shiga yajin aikin dindindin, amma a irin halasci irin na mu, za mu cigaba da kula da marasa lafiya da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, amma ba za mu sake karbar wani mara lafiya a asibiti ba, kuma zamu cigaba da sallamar wadanda aka kwantar saboda ba zamu iya kulawa da su ba.” Inji shi.

Tun a watan Oktoban 2017 ne gwamnatin jahar Kaduna tare da kungiyar ARD suka shiga wata yarjejeniyar warware dukkanin rikicin dake tsakaninsu, tare da iyakance iya lokacin da za’a dauka ana aiwatar da alkawurran domin cimma yarjejeniyar.

A cewar kungiyar, ta cika alkawarinta, amma gwmanati ta gaza a bangarenta, duk da cewa sun tuntubi gwamnatin jahar Kaduna a ranar 25 ga watan Nuwambar 2019, inda suka basu wa’adin watanni uku don su cika alkawarin, amma gwamnatin bata cika alkawarin ba.

“Sai da gwamnati ta tabbatar za mu shiga yajin aiki, shi ne ta kafa wata kwamiti a ranar 27 ga watan Feburairu, inda shugaban kwamitin ya rokemu mu daga musu kafa zuwa ranar 3 ga watan Maris an shekarar 2020 don ji daga gare su, amma har yanzu shiru.

“Don haka muka yanke hukuncin shiga yajin aiki tun da gwamnatin ta gagara cika alkawarinta.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa game da bullar annobar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya gaba daya, do haka ya yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’I na musamman.

Sultan ya yi kira ga Musulmai su dage da tsafta tare da bin duk wasu hanyoyin tsaftace kawunansu don kauce ma yada cutar Coronavirus, sa’annan ya yi kira ga Malamai da limamai su cigaba da wayar da kawunan jama’a akan cutar a dukkanin salloli biyar na kowanne rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel