Boko Haram: Yan sanda 4, masu farin hula 2, suka rasa rayukansu a harin Damboa

Boko Haram: Yan sanda 4, masu farin hula 2, suka rasa rayukansu a harin Damboa

A yau Laraba ne 4 ga watan Maris 2020, yan boko Haram su kai hari barikin sojoji inda suka kashe yan sanda hudu da wasu masu farar hula biyu a Jihar Borno, cewar majiyar ja’mian tsaro ga AFP.

Yan boko haram din da ake zargi, sun kai hari ne barikin sojojin akan manyan motoci dauke da bindigogi a garin Damboa.

“Mun rasa yan sanda hudu da masu farar hula biyu da suka shigarwa sojojin fada yayinda yan ta'addan suka kawo hari,”A cewar wani soja.

Wani dan kato da gora, Ibrahim Liman ya tabbatar da hakane bayan ya taimakawa sojojin a artabun.

Wani mazaunin kauye, Modu Malari yace yan ta’addan suka kawo hari da manyan bindigogi amma sojoji suka ci nasarar korasu daga garin bayan an yi musayar wuta na tsawon awanni biyu.

Sun raunana fiye da mutane 50 a yayinda suke ta kawo farmaki, yayinda wasu suka gudu gidaje mafi kusa da wurin.

Kauyen Damboa yana kusa da dajin Sambisa inda yan ta'addan Boko Haram suke boyewa suna kai hari kauyuka da barikin sojoji.

Boko Haram: Yan sanda 4, masu farin hula 2, suka rasa rayukansu a harin Damboa
Boko Haram: Yan sanda 4, masu farin hula 2, suka rasa rayukansu a harin Damboa
Asali: Facebook

A wani labarin daban, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum yace ya kasa tsayar da hawayena yayinda yake kallon yadda yan gudun hijira suke layin amsar kayan masarufi.

Zulum ya bayyana hakane yayinda ake rabawa yan sansanin IDP 19,000 kayan masarufi ranar talata, a Gajiram, hedkwatar karamar hukumar Nganzai dake Jihar.

Gwamnan wadda ya sa ido yayinda ake rabawa yan gudun hijira kayan, ya karaya akan matsanancin halin da masu tayar da kayar bayan Boko Haram suka sanyasu a ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel