'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 5, malami da kuma masu gadi 2 a jihar Neja

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 5, malami da kuma masu gadi 2 a jihar Neja

'Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata biyar, malami daya da kuma masu gadin makarantar Tular Academy da ke Moruba a karamar hukumar Mariga da ke jihar Neja.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, ya bayyana hakan ne a yayin da jami'an 'yan sanda da sojoji suka kai ziyara makarantar bayan aukuwar lamarin.

Usman ya ce lamarin ya faru a ranar 1 ga watan Maris wajen karfe 1:45 na dare a farfajiyar makarantar.

Ya ce ziyarar ganin halin da ake ciki da rundunar 'yan sandan suka kai, sun yi ta ne don sanin salon tsaron da zasu assasa a makarantar.

Ya ce tuni dai rundunar ta watsa jami'anta don ceto wadanda aka sacen.

"Tuni muka tura runduna ta musamman masu yaki da fashi da kuma garkuwa da mutane a yankunan don ceto wadanda aka sacen," kwamishinan ya ce.

Ya ce duk da girman yankin, jami'an tsaro na kokarin shawo kan matsalar tsaron.

'Yan bindiga sun yi awwon gaba da dalibai 5, malami da kuma masu gadi 2 a jihar Neja

'Yan bindiga sun yi awwon gaba da dalibai 5, malami da kuma masu gadi 2 a jihar Neja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Kamar yadda ya ce, jami'an tsaron hadin guiwa na jiha da jiha sun taimaka ba kadan ba wajen nasarorin da ake samu wajen yakar rashin tsaro a jihar.

Usman ya jajanta yadda 'yan bindigar suka yi amfani da matsalar sadarwa a yankin kuma suka kwashe yaran 'yan makaranta.

Yayi bayanin cewa matsalar sadarwan ce ta sa sai bayan sa'o'i 24 da aukuwar lamarin rundunar 'yan sandan ta samu labari.

Ya kara da dora laifin da karancin tsaro da makarantar ke fama da shi.

Kwamishinan ya kara da cewa babu wani matsi ko damu da zai sa rundunar ta kasa sauke nauyinta na kare rayuka da kadarorin jama'a a jihar.

Ya kara kira ga jama'ar yankin karkarar da su gaggauta kaiwa hukumomin tsaro rahoton mutane ko kungiyar da basu yadda dasu ba.

Ya kara da shawartar mazauna karkarar da su kafa kungiyoyin sintiri da taimakon kai da kai don tantancewa daga ofishin 'yan sandan Mariga don tallafawa jami'an tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel