Zulum ya kasa tsayar da hawayensa yayinda yake rabawa yan gudun hijira kayan masarufi

Zulum ya kasa tsayar da hawayensa yayinda yake rabawa yan gudun hijira kayan masarufi

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum yace ya kasa tsayar da hawayena yayinda yake kallon yadda yan gudun hijira suke layin amsar kayan masarufi.

Zulum ya bayyana hakane yayinda ake rabawa yan sansanin IDP 19,000 kayan masarufi ranar talata, a Gajiram, hedkwatar karamar hukumar Nganzai dake Jihar.

Gwamnan wadda ya sa ido yayinda ake rabawa yan gudun hijira kayan, ya karaya akan matsanancin halin da masu tayar da kayar bayan Boko Haram suka sanyasu a ciki.

Yace: “Yaushe mutanenmu zasu dena layin amsar kayan masarufi. Ina kira a gareku da ku bada hadin kai ga jami’an tsaro domin su samar mana zaman lafiya a kasar mu yadda mutanenmu zasu koma ayyukan nomansu."

“Ba zamu iya cigaba da dogara akan abincin taimako ba don mu rayu, Ku yi tunanin irin ayyukan zamu iya yi da kudaden da muke zubawa wajen sayen kayan masarufi."

Zulum ya kasa tsayar da hawayensa yayinda yake rabawa yan gudun hijira kayan masarufi
Zulum ya kasa tsayar da hawayensa yayinda yake rabawa yan gudun hijira kayan masarufi
Asali: Facebook

Zulum ya jaddada niyyarsa wajen kawo karshen ta'addanci a jihar domin samar da kwanciyar hankali da natsuwa.

Yayi kira ga dattawa da jama’an gari su baiwa jami’an tsaro hadin kai wajen basu da bayanai akan wani kai da komon da basu yadda dashi ba, da kuma abubuwan da suke faruwa a unguwanninsu.

NAN ta ruwaito cewa an baiwa kimanin matan aure 11,300 kayan sawa da N5,000, yayinda aka baiwa mazaje 7,800 buhun shinkafa da na masara tare da lita uku na man girki.

A bangare guda, yan boko Haram su kai hari barikin sojoji inda suka kashe yan sanda hudu da wasu masu farar hula biyu a Jihar Borno, cewar majiyar ja’mian tsaro ga AFP ranar Laraba.

Yan boko haram din da ake zargi, sun kai hari ne barikin sojojin akan manyan motoci dauke da bindigogi a garin Damboa.

“Mun rasa yan sanda hudu da masu farar hula biyu da suka shigarwa sojojin fada yayinda yan ta'addan suka kawo hari,”A cewar wani soja.

Wani dan kato da gora, Ibrahim Liman ya tabbatar da hakane bayan ya taimakawa sojojin a artabun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel