Kudade kan iya kara yaduwar cutar Coronavirus - WHO

Kudade kan iya kara yaduwar cutar Coronavirus - WHO

Kungiyar kiwon Lafiya ta duniya WHO ta shawarci jama’a da su rinka amfani da naurorin zamani wajen bukatunsu na kudi, domin kudi kan iya jawo yaduwar coronavirus.

Cutar Coronavirus zata iya zama akan kudi na tsawon kwanaki, Kungiyar kiwon lafiya tayi gargadi a daren Litinin.

Cutar Coronavirus zata iya yaduwa ta hanyar abubuwan da suke dauke da cutar da kuma haduwa da wadanda suke dauke da cutar, cewar kungiyar WHO.

"Domin hana yaduwar cutar, mutane su rinka amfani da naurorin zamani domin gudanar da bukatunsu na kudi bayan haka kuma su wanke hannayensu bayan sun taba kudin" cewar mai Magana da yawun kungiyar WHO.

Bankin Kasar Ingila ta gano cewa kudi kan iya daukar kananan kwayoyin cuta, kuma ta karfafa akan yawan wanke hannaye.

Kudade kan iya kara yaduwar cutar Coronavirus - WHO
Kudade kan iya kara yaduwar cutar Coronavirus - WHO
Asali: UGC

A watan baya, bankin kasar Koriya da China sun fara tsaftacewa da killace kudaden da akayi amfani dasu domin takaita yaduwar annobar cutar.

A wata majiya daga bankin kasar Ingila ta bayyana cewa ba wani shirin yin haka a kasar.

Wani mai magana da yawun bankin Ingila ya bayyanawa jaridar TELEGRAPH cewa: “Ba kamar wata farfajiya da mutane da yawa suke hulda ba, kudade suna daukar kananan kwayoyin cuta."

“Munsan kudi na zuwa hannaye daban-daban kuma zai iya daukar ko wani irin kwayar cuta."

“Muna shawartar mutane dasu wanke hannayensu a yayin da suka gama hulda da kudi, kuma su kauracewa taba fuskokinsu. Idan akwai dama su rika amfani da naurori,"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel