Amurka za ta bada kyautar N2.5bn ga wanda ke da bayanni kan Shekau

Amurka za ta bada kyautar N2.5bn ga wanda ke da bayanni kan Shekau

- Kasar Amurka ta saka kyautan kudi Dalla miliyan 7 a kan shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau

- Amurkan ta ce za ta bayar da kudin ga duk wanda ya bayar da bayannai da suka yi dalilin kama Shekau

- A cewar rahoton, an kuma saka kyautar Dalla miliyan 5 a kan wanda ya bayar da bayani a kan shugabanin ISIS uku

Wani rahoto a sashin Shari'a na Amurka ya fitar ya ce an ware kyautar zunzurutun kudi Dalla miliyan 7 da kimanin Naira Biliyan 2,52 ga duk wanda ya bayar da bayanai da ya yi sanadin kama shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da ya dade yana addabar Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

PM News ta ruwaito cewa an saka kyautan kudin ne a kan dukkan shugabannin kungiyoyin ta'adda da Amurka ke neman su ruwa a jallo.

Kasar ta Amurka ta ce: "Dukkan gwamnatoci da al'umma suna da rawar da za su taka domin ganin an hukunta 'yan ta'adda tare da kare afukuwar ayyukan ta'addanci."

DUBA WANNAN: Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja

Legit.ng ta gano cewa an fitar da sanarwar ne a shafin Hukumar Shari'a ta Amurka mai amfani da harshen Faransanci a karkashin shirin bayar da kyauta domin tabbatar da adalci.

Sanarwar ya bayyana lambobin da duk wanda ke da ra'ayi kuma ke da bayyanan da zai bayar zai tuntuba kamar haka Whatsapp: +1 202 975 9195 sai kuma Telegram: @RFJ_Francais_bot.

A cewar sanarwa ba a san dalilin da yasa hukumar ta yi amfani da sashin ta na Faransanci ba wurin fitar da sanarwar amma ba ta saka a na Turanci ba.

A shafin ta na Turanci da ta bude a ranar 27 ga watan Fabrairu, tsarin na biyan la'ada ga wanda suka bayar da bayanai ya kuma fitar da sanarwar bayar da la'adan Dalla Miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayyanai a kan shugabanin ISIS uku da kuma Dalla miliyan 6 a kan wasu shugabannin kungiyoyin ta'adda na AQAP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel