'Yan darikar 'Faidha' da ake zargi da yin wakar batanci ga Annabi sun tsallake rijiya da baya

'Yan darikar 'Faidha' da ake zargi da yin wakar batanci ga Annabi sun tsallake rijiya da baya

Mutanen wani gida da ke unguwar Sharifai a cikin birnin Kano sun sha da kyar bayan wasu fusatattun matasa sun kai farmaki unguwar tare da yunkurin kone musu gida bisa zarginsu da yin wata wakar batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A cewar jaridar Daily Trust, wani bincike ya gano cewa wani dan gidan mai suna, Yahaya Sharif Aminu, shine ya rera wakar da a cikinta aka yi amfani da kalaman batanci a kan manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi).

Wakar, wacce nan da nan ta zagaya gari bayan an wallafa ta a dandalin sada zumunta, ta fusata matasan da suka yi yunkurin kone gidan su mawakin kurmus.

An gano cewa matashin mawakin, Yahaya Sharif Aminu, mabiyin mazhabar 'Faidha' ne a cikin darikar Tijjaniyya. 'Yan 'Faidha' sun yi kaurin suna wajen fifita soyayyar Shaikh Ibrahim Nyass a kan soyayyar annabi Muhammad (SAW) da Allah.

Albarkar mata da kananan yara da ke cikin gidan yasa matasan basu cinna masa wuta ba, kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust.

'Yan darikar 'Faidha' da ake zargi da yin wakar batanci ga Annabi sun tsallake rijiya da baya
Fusattun matasa suna rushe gidan su matashi Yahaya
Asali: Facebook

Wani shaidar gani da ido, Rabi'u Muhammad, ya bayyana cewa an kwashe mutanen gidan tare da boye su a wani gidan daban.

Wasu mazauna unguwar Sharifai sun bayyana matukar kaduwa da mamaki a kan wakar da matashin ya wallafa.

DUBA WANNAN: Imo: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba hukuncin kwace kujerar gwamnan PDP

Malam Murabba'i, wani makwabci ga Yahaya, ya shaida wa manema labarai cewa basu yi tsammanin matashin zai aikata haka ba, saboda bashi da yawan hayaniya. Ya bayyana shi da mai shiru - shiru da babu alamun zafin akida a tare da shi duk da kowa ya san cewa dan darikar Tijjaniyya.

Wannan ba shine karo na farko da mabiya 'Faidha' suka fara wallafar wakar da ta kawo hargitsi a Kano ba. Ko a cikin shekarar 2015 sai da gwamntin jihar Kano ta gurfanar da wani matashi, Abdul Nyas, a gaban kuliya bayan ya wallafa wata wakar batanci da rashin girmama Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel