Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Wasu matasa sun dira ofishin Hisbah a ranar Laraba a kan zargin wata waka da aka yi na cin mutuncin manzon tsira Annabi Muhammad (SAW).

Masu zanga-zangar da ke dauke da takardu masu rubutu sun yi ikirarin cewa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suna jan kafa wurin daukan mataki a kan lamarin.

Jagorar masu zanga-zangan, Idris Ibrahim (da aka fi sani ba Baba Idris) ya ce sun zo ne su sanar da gwamnati ta dauki mataki a kan lamarin idan kuma ba haka ba su za su dauki matakin da kansu.

Mista Ibrahim ya ce a baya an samu afkuwar irin wadannan abubuwan a jihar kuma hukumomin tsaro ba su dauki matakan da ya dace a kai ba.

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad
Source: Twitter

Wani Yahaya Sharif-Aminu ne ya yi wata waka da ke dauke da wasu kalamai da ake zargin na batanci ne ga Annabi Muhammadu (SAW). Hakan ya yi sanadiyar rushe gidan mawakin kuma ya tsere daga unguwar.

DUBA WANNAN: Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja

A ranar Juma'a da ta gabata, wasu fusatattun matasa sun bankawa gidan mawakin wuta a rukunin gidaje na Sharifai da karamar hukumar Kano Municipal a kan wakar.

Da ya ke jawabi ga masu zanga-zangan, kwamandan Hisbah na Kano, Harun Ibn-Sina ya ce jami'an hukumar suna bincike a kan lamarin kuma har sun kama iyayen mawakain an tsare su.

Kazalika, wakilin kwamishinan 'yan sandan jihar, Habu Sani ya fadawa masu zanga-zangar cewa 'yan sanda suna bin sahun mawakin domin su kama shi.

Wakilin shugaban 'yan sandan da ya ce sunansa Hamza ya bukaci masu zanga-zangan su zama masu biyaya ga doka su kyalle hukumomin tsaro su yi aikinsu.

Ya tabbatar wa masu zanga-zangan cewa za a hukunta mawakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel