Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 83 da haihuwa

Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 83 da haihuwa

- Shugaba Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo murna zagayiwar ranar haihuwarsa

- Tsohon shugaban kasar zai yi bikin cika shekaru 83 a duniya a ranar Alhamis 5 ga watan Maris a Abeokuta babban birnin jihar Ogun

- A sakon da ya aike masa, Buhari ya bayyana Obasanjo a matsayin mutum kai kwazo da jarumta da ya yi wa al'umma hidima

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a kan bikin cikarsa shekaru 83 a duniya.

Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasar ta bakin mai bashi shawara na musamman a kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina, ya taya Obasanjo murna a kan rayuwa mai kyau da ya yi da yi wa Najeriya, Afrika da duniya hidima.

Sanarwar ta ce: "Shugaba Buhari yana taya iyalai, abokai da na hannun daman tsohon shugaban kasa a yayin da suke taya shi murna. Hidima da ayyuka da Cif Obasanjo ya yi wa nahiyar Afirka abin yabo ne tare da jajircewarsa wurin wanzar da demokradiyya a kasashe da yawa.

Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 83 da haihuwa

Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 83 da haihuwa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja

"A yayin da tsohon shugaban kasar ke murnar ranar zagayowar ranar haihuwarsa, Shugaba Buhari yana addu'a Allah ya bashi tsawon rai da lafiya da karfi da zai cigaba da yi wa kasarsa da nahiyarsa hidima."

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa tsaffin shugabannin kasashen Afirka za su hallarci dakin karatu na Olusegun Obasanjo a Abeokuta a jihar Ogun domin bikin cikarsa shekaru 83 a duniya.

An ruwaito cewa tsohon shugaban kasar zai cika shekaru 83 a ranar Alhamis 5 ga watan Maris kuma an shirya bukukuwa da dama da za a gudanar a Cibiyar Tsaro da Sulhu ta (CHSD).

Har ila yau, Obasanjo ya bayyana cewa ya zama dole gwamnatin Najeriya ta kawo karshen rashin tsaro da ake fama da shi.

Ya ce ya zama dole kowa ya bayar da gudunmawa wurin tabbatar da tsaro a kasar.

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne yayin wata ziyara ta musamman da ya kaiwa Archibishop na Canterbury, Archibishop Justin Welby a Abeokuta ya jihar Ogun inda Obasanjo ya ce ya zama dole dukkan 'yan Najeriya su yinaiki da addu'a don samun zaman lafiyan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel