Gwamnatin tarayya ta kammala manyan tituna a cikin jami’ar Bayero ta Kano

Gwamnatin tarayya ta kammala manyan tituna a cikin jami’ar Bayero ta Kano

Ministan ayyuka da gidaje na Najeriya, Babatunde Raji Fashola ya mika ma hukumar jami’ar Bayero ta Kano wasu manyan tituna da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta kammala gudanar da gyaransu a cikin jami’ar.

Premium Times ta ruwaito Fashola, wanda ya samu wakilcin kwanturolan ayyuka a jahar Kano, Idi Saje ya bayyana manyan ayyukan jin dadi a matsayin muhimman gudunmuwa wajen cigaban ilimi a Najeriya.

KU KARANTA: Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

Gwamnatin tarayya ta kammala manyan tituna a cikin jami’ar Bayero ta Kano
Gwamnatin tarayya ta kammala manyan tituna a cikin jami’ar Bayero ta Kano
Asali: Facebook

“Muna kokarin cike gibin da aka samu a bangaren samar da manyan ayyuka ta hanyar gyare gyare, garambawul, sabuntawa da kuma gina sababbin hanyoyi, wanda a yanzu haka ya kai ga makarantu.

“A yanzu mun kammala ayyuka 18 cikin 43 da muke gudanarwa a cibiyoyin ilimi a Najeriya, don haka a yau mun mika wannan muhimmin aiki ga jami’ar Bayero ta Kano a matsayin gudunmuwa ga cigaban ilimi.” Inji shi.

A yayin taron, shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Yahuza Bello ya karrama ministan da lambar yabo, sa’annan ya bayyana cewa aikin titin zai rage radadin da al’ummar jami’ar suke fuskanta, kuma zai sa dalibai da malamai su dinga shiga aji akai akai tare da rage aukuwar haddura a kan hanyar.

Farfesa Yahuza ya bayyana jin dadinsa da yadda aka gudanar da aikin titunan wanda yace har da magudanan ruwa aka gina musu, ya shaida ma ministan cewa sun yaba da ingancin aikin, kuma zasu tabbatar da sun kula da su tare da amfani dasu yadda ya kamata.

Shi ma shugaban sashin kula da ayyuka na jami’ar BUK, Muhammad Gazzali ya tabbatar da ingancin aikin, inda yace za’a dade ana moransu. Haka zalika wakilin kamfanin da ta gudanar da kwangilar, Tours Nigeria Limited, Abideen Abdulazeez ya gode ma ministan bisa samun kudadensu a lokacin daya kamata.

A wani labarin kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta fara gudanar da tantance ma’aikata da kuma bakin dake ziyartar fadar dake babban birnin tarayya Abuja biyo bayan samun bullar annobar cutar Coronavirus mai suna COVID-19 a Najeriya a ranar juma’ar da ta gabata.

Jami’an kiwon lafiyan suna amfani da na’urar gwada zafin jikin mutum domin gwajin yanayin zafin ma’aikatan Villa da kuma baki, daga cikin wadanda aka yi ma wannan gwaji a ranar Talata akwai ministan kwadago, Chris Ngige wanda ya isa fadar da misalin larfe 4:50 na rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel