Motar 'yan kungiyar Lobi stars ta yi gobara, wasu 'yan wasa sun jikkata

Motar 'yan kungiyar Lobi stars ta yi gobara, wasu 'yan wasa sun jikkata

'Yan wasan kwallon kafa na kungiyar Lobi stars da dama sun jikkata a ranar Litinin bayan babban motarsu ta yi gobara a hanyarsu na dawowa daga wasa a Ilorin.

Kungiyar da ke Makurdi ta yi nasarar doke kungiya mai masaukin baki ta Kwara United 1-0 a wasan da suka buga a ranar Lahadi a filin wasanni na garin Ilorin.

The Punch ta ruwaito cewa 'yan wasan suna dab ta isa gida ne lokocin da motar da kama da wuta a Nakka Road da ke wajen Makurdi a jihar Benue.

Motar 'yan kungiyar Lobi stars ta yi gobara, wasu 'yan wasa sun jikkata

Motar 'yan kungiyar Lobi stars ta yi gobara, wasu 'yan wasa sun jikkata
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda mace mai shekaru 70 ta yi wa mafarauta jagora tsirara suka shiga daji suka kashe 'yan bindiga 40 a Neja

Ba a san ainihin abinda ya yi sanadin gobarar ba a lokacin rubuta wannan rahoton amma majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa 'yan wasa da dama sun samu rauni yayin da suke kokarin ficewa daga motar bus din da ta kama da wuta cikin 'yan mintuna.

Mataimakin kocin na Lobi stars, Lawal Abiodun ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa, "wasu 'yan wasan sun kuje amma babu wanda ya samu mummunan rauni. Dukkan 'yan tawagan suna nan lafiya. Mun gode wa Allah."

A wata bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta, An gano dan wasan Lobi stars, Musa Najare yana bayyanin yadda lamarin ya faru cikin fargaba.

An jiyo shi yana cewa, "Ku kalli motar mu, ku kalli motar 'yan Lobi stars, Allah mun gode maka, Yesu muna maka godiya. Suna na Musa Najare, ku kalli abinda ke faruwa da mu a halin yanzu. Wannan shine motar mu. Wannan shine motar Lobi stars. Mun gode maka Yesu saboda ceton mu da kayi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel