Zafin Nigeria kan iya takaita yaduwar Coronavirus - Likita

Zafin Nigeria kan iya takaita yaduwar Coronavirus - Likita

Wata Likitar kananan kwayoyin cututtuka, Adeola Fowotade, yace sauyin yanayi na zafi a Nigeria kan iya taimakawa wajen dakile da yaduwar cutar Coronavirus.

Fowotade, mai aiki a babban asibitin UCH dake birnin Ibadan, ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN ne a Ibadan.

Bisa ga bayaninta, wasu daga cikin gwanaye suna tunanin Coronavirus zata iya dabi’antuwa da cutar mura, wacce take aukuwa duk shekara a yanayin sanyi, idan haka ya tabbata, zafin Nigeria kan iya hana yaduwar coronavirus.

Tace: “Muna kyautata zaton cewa idan Covid-19 cutar layin numfashi ne, to zai iya bin sahun hakan. Akwai yiwuwan idan yanayi ya sauya a kasashen da ke fama da sanyo yanzu, abubuwan zau yi sauki.”

“Amma mu masu yanayi mai zafi, muna imanin cewa nan ba da dadewa ba cutar zai gushe.”

“Dalili shine kwayar cutar diga takeyi kuma saboda haka ba zata iya tafiya mai nisa ba. Kasancewarta haka, ba zatayi rayuwa cikin zafi ba.”

Amma ta yi kira ga kowa musamman ma’aikatan kiwon lafiya su cigaba da mayar da hankali wajen tsafta da lura.

Zafin Nigeria kan iya takaita yaduwar Coronavirus - Likita

Zafin Nigeria kan iya takaita yaduwar Coronavirus - Likita
Source: Twitter

KU KARANTA: Zaben Bayelsa: Degi Biobara na yunkurin kashe kansa - Minista Man fetur

A bangare guda, Gidauniyar alhaji Aliko Dangote (ADF) tayi alkawarin ba da gudunmuwar milyan dari niyu (N200m) domin taimakawa gwamnatin tarayya wajen takaita yaduwar cutar coronavirus a Najeriya.

Zuwaira Yusuf, Shugabar gidauniyar, a wani jawabi ranar Talata a Legas, ta bayyana cewa taimakon yana daya daga cikin muhimman manufofin gidauniyar.

Zuwaira tace gidauniyar ta tanadi N124m domin taimakawa asibitoci wurin gwaji, kula da kawar da cutar a hanyoyin shiga Najeriya domin tabbatar da lafiyar kasa baki daya.

A cewarta, gidauniyar zata samar da cibiyoyin bincike kan cutar na kimanin N36m domin taimakawa gwamnati.

Tace har ila yau, gidauniyar zata bada N48m domin kula da wadanda suka kamu da cutar da kuma horar da masu kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel