Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Aminu Aliyu

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Aminu Aliyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta tare da yin ta'aziyya ga iyalan Aliyu a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.

Shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyyar ne ta wata takarda da babban mai bayar da shawara ga shugaban kasar a kan yada labarai, Garba Shehu, a ranar Litinin a garin Abuja.

Shugaban kasar yayi ta'aziyyar ne ga Magaji Aliyu, shugaban kwamitin wutar lantarkj na majalisad tarayya tare da abokin gwagwarmayar siyasarsa, Farouk Aliyu a kan rashin.

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Aminu Aliyu

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Aminu Aliyu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

Ya yi kira garesu da su dau hakuri tare da tunawa cewa mamacin mai cike da tsoron Allah din ya rasu ne yana hidimtawa yankinsa da al'umma.

Buhari ya hadu da gwamnati tare da jama'ar Jigawa wajen makokin Aliyu.

Ya yi addu'ar Ubagiji ya sanya wa iyalan Aliyu salama da hakuri tare da duk wadanda mutuwar ya shafa.

Yana fatan Ubangiji yasa ya huta kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito.

A wani labarain, kun ji cewa Majalisar Wakilai na tarayya za ta dage zamanta na tsawon makonni biyu saboda fargabar yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus a Majalisar ta tarayya.

Majalisar ta cimma matsayar dakatar da zamanta ne bayan da Mista Josiah Idem ya gabatar da bukatar yin hakan a zauren majalisar a ranar Talata kuma sauran takwarorinsa suka amince da hakan.

Shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu, ya kara neman a dakatar da zaman majalisar na makonni biyu domin a bawa masana lokaci su shirya wa yadda za a kare yaduwar cutar a harabar Majalisar na Tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel