Coronavirus: Har yanzu gwamnati na neman wadanda suka hau jirgi tare da dan Italiya ya kawo cutar Najeriya
Har ila yau, gwamnatin tarayya tana cigaba da kokarin gano fasinjoji 155 da suka hau jirgi zuwa Nigeria tare da dan kasar Italiyan da aka tabbatar yana dauke da cutar coronavirus da ya shigo kasar.
Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana hakane ga manema labarai a Abuja inda yace fasinjoji 156 suka hau jirgi tare da dan kasar Italiyan.
Daily Trust ta ruwaito cewa sabanin abinda ake samu daga wasu kasashe, ba’a bayyana sunan dan Italiyan mai dauke da cutar ga Jama’a ba.
Ministan yace ba’a gano wasu daga cikin fasinjojin da suka hau jirgi tare da dan Italiyan ba saboda ba’a samu bayanai daga garesu ba yadda ya kamata
Yace: “Ba za mu iya kayyade adadin wadanda ya hadu da su ba, Amma wadanda muke da tabbaci akansu sune fasinjoji 156 da suke tare dashi a jirgin, kuma ana bibiyansu, ana magana dasu kuma suna bada hadin kai."
“Muna fuskantar kananan kalubale. Wasu daga cikinsu sun bada lambobin waya mara aiki ko kuma idan an kira aji a kashe. Akwai kuma wadanda basu da wayar, ko kuma sabbi ne a kasar."
“Ba’a musu rajista da wani kamfanin wayar tarho ba, amma akwai hanyoyin da za’a nemosu. Wadand kuma a suka shigo dan ziyarar kwana daya ko biyu tuni sun bar kasar,”a cewar sa.
Ehanire yace tun lokacin da aka tabbatar da bullowar cutar ta farko, gwamnatin tarayya ta sa kai dan ganin ta takaita yaduwar cutar.yace har izuwa jiya ba’a samu Karin sabbin wadanda suka kamu da cutar ba a Nigeria.

Asali: Twitter
A bangare guda, Akalla mutane 3000 sun mutu kawo yanzu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya.
Kawo yanzu kimanin mutane 80,000 suka kamu da wannan cuta a fadin kasar Sin da kuma kimanin 4000 a ksar Koruya ta kudu.
Bullowar cutar a kasar Koriya ta kudu, inda itace mafi girma bayan Kasar Sin da cutar ta fito.
Ga jerin kasashe 66 da cutar ta bulla yanzu:
1. Afghanistan
2. Algeria
3. Australiya
4. Austria
5. Azerbaijan
6. Bahrain
7. Belgium
8. Brazil
9. Cambodiya
10. Sin
11. Czech
12. Canada
13. Croatia
14. Denmark
15. Dominica
16. Ecuador
17. Misra
18. Faransa
19. Geogiya
20. Jamus
21. Greece
22. Hong Kong
23. Iceland
24. Indiya
25. Indonisiya
26. Iraqi
27. Iran
28. Izraila
29. Italiya
30. Japan
31. Kuwait
32. Lebannon
33. Lithunia
34. Luxewmborg
35. Macau
36. Malayssiya
37. Mexico
38. Nepal
39.Holand
40. New Zealand
41. Najeriya
42. North Macedoniya
43. Norwway
44. Oman
45. Pakistan
46. Fillibin
47. Tunisiya
48. Jordan
49. Qatar
50. Romaniya
51. Rasha
52. San Marino
53. Singapore
54. Saudiyya
55. Koriya ta kudu
56. Sifen
57. Sri Lanka
58. Senegal
59. Sweden
60. Switzerland
61. Taiwan
62. Thailand
63. UAE
64. Birtanniya
65. Amurka
66. Vietnam
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng