Zaben Bayelsa: Degi Biobara na yunkurin kashe kansa - Minista Man fetur

Zaben Bayelsa: Degi Biobara na yunkurin kashe kansa - Minista Man fetur

Karamin Ministan man fetir, Timipre Sylva, a ranar Litinin ya bayyana cewa soke nasarar zababben mataimakin gwamnan jihar bayelsa, Biobarakuma Degi-Eremiengo, da kotun koli tayi ya ja yana yunkurin kashe kansa.

Sylva, ya bayyana hakane a wani shiri na Sunrise daily a tashar Channels inda ya cewa hukuncin kotun koli akan zaben gwamnan jihar Bayelsa bai kamata ba.

Kotun kolin ta rushe nasarar da dan jam’iyyar APC ya samu a zaben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon, a ranar 13 ga watan Febrairu 2020, sakamakon sabani da aka samu a satifikate din mataimakin da aka kaddamar wa hukumar gudanar da zabe ta kasa.

Sylva yace: “Ina fama da tsohon mataimakin gwamna wadda yake kokarin kashe kanshi. Wannan al’amarin rai da mutuwa ne. A kullum sai na kira in tabbatar da bai yiwa kanshi komai ba."

“Bayan ka gina rayuwarka da mutuncinka kawai sai wani ya zo ya wargaza komai yace satifikate dinka ma kirkirar sa kayi wadda zai iya jawo maka kisan kai."

“Idan wai dan ka kai kara kotu kana kalubalantar satifikate din wani, wannan daban ne. Amma idan kace kirkirar satifikate din yayi kuma baka ji daga bakinshi ba, toh baka tabbatar da komai ba."

“Kai ba zuwa makaranta ko jami’ar da mutum halarta kayi ba,ka tabbatar da kirkirar satifikate din yayi amma kayi hukunci akai. Wannan abin bakin ciki ne kuma yana da hadari.”

A bangare guda, Kotun koli ta y watsi da bukatar sake duba hukuncin da ta yanke na kwace kujerar gwaman jihar Imo daga hannun Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP tare da bayar da umarnin mika ta ga Hope Uzodinma na jami'iyyar APC.

Da take yanke hukunci ranar Talata a kan bukatar sake duba hukuncin, kotun; mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa (CJN), Tanko Muhammad, ta bayyana cewa ba ta da ikon sake zama domin sauraron daukaka karar neman ta sake duba hukuncin da ta yanke da kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel