Yadda wani minista ya durkusa har kasa ya gaisar da jarumar fim

Yadda wani minista ya durkusa har kasa ya gaisar da jarumar fim

- Wani hoton ministan ayyuka na musamman na Najeriya da fitaciyyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood wato Regina Daniels na ta yawo a kafafen sadarwa

- An hango ministan dai ya durkusa yana mikawa fitacciyar jarumar hannu a matsayin suna gaisawa, sai dai kuma wannan gaisuwar tayi daban domin kuwa ministan ya rankwafa ne sannan ya mika mata hannu

- Hakan ya jawo kace-nace sosai a kafafen sadarwa, inda mutane kowa ke fadar albarkacin bakinsa kan wannan lamari

Wani hoto da yake ta faman yawo a shafukan sada zumunta na hamshakin mai kudin nan Ned Nwoko da matarsa fitacciyyar jarumar fina-finan Nollywood na kudancin Najeriya Regina Daniels, ya jawo kace-nace, yayin da aka ga Sanata Goerge Akume, wanda a yanzu yake da mukamin ministan ayyuka na musamman.

Hoton dai ya nuna lokacin da ministan ya ragwafa yake gaishe da fitacciyar jarumar wacce take tsaye kusa da mijinta su kuma da abokanan shi suna dariya abinsu.

Yadda wani minista ya durkusa har kasa ya gaisar da jarumar fim
Yadda wani minista ya durkusa har kasa ya gaisar da jarumar fim
Source: Facebook

Ga dai abinda wasu daga cikinsu ke cewa:

Budurwa mai suna Crazina Sally cewa tayi: "Mijinta shi kanshi dariya yake saboda wannan abu da ministan yayi," Wani kuwa mayar mata da martani yayi da cewa "Lamarin nasu ya koma tamkar wasan kwaikwayon barkwanci."

Haka shi ma wani mai suna Jila Barnabas cewa yayi: “Shin Sanatan yana so ya durkusa mata ne ko yaya?”

Wata kuwa mai suna Teryem Tarker cewa tayi: “Duk macen da take da mutucin da tausayi dole manya su girmamata, hatta lokaci zai tafi mata yadda take so.”

KU KARANTA: Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya

Wannan dai shine karo na farko da aka taba ganin hakan ta faru a Najeriya, inda kowa ya san cewa shugabannin Najeriya na da matukar son girma.

To sai dai kamar yadda da yawa suka bayar da sharhi cewa ministan abokine ga mijin jarumar, hakan bai saka ya rankwafawa mijin ba wanda yake shine hamshakin mai kudin.

Wasu kuwa sun bayyana cewa ministan yayi hakane saboda neman kudi, to koma dai menene dalilinsu, su ka dai suka sani.

A daya bangaren kuma, wani farfesa dan Najeriya mai suna Farfesa Maduike Ezeibe ya sanar da cewa ya samo maganin cutar Coronavirus da zazzabin Lassa, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Farfesan a fannin 'Virology' a jami'ar Michael Okpara ta aikin noma da ke Umudike, ya taba ikirarin samo maganin cuta mai karya garkuwar jiki. Ya tabbatar da cewa tunda ya samar da maganin cuta mai karya gakuwar jikj, cutar Coronavirus za ta zama tarihi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel