Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta

Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta

Mataimakin gwamnan jahar Kogi, Edward Onoja ya koma makaranta don samun digiri na biyu da digirin digirgiir fannin zaman lafiya da warware rikice rikice a jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Lokoja.

TheCables ta ruwaito Onoja ya bayyana haka ne a shafukansa na dandalin sadarwar zamani, inda yace a ranar Litinin ya fara daukan darasi, ya kara da cewa makasudin komawarsa makaranta shi ne don a yanzu duniya na bukatar kwararru wajen kashe wutar rikice rikice.

KU KARANTA: Rikicin cikin gida: Sabon shugaban ISWAP ya halaka manyan kwamandoji 5

Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta
Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta
Asali: UGC

Mista Onoja ya kara da cewa yana fatan zai kammala karatun digirin digirgir zuwa shekarar 2023.

“Na koma makaranta don karatun digiri na biyu, a bangaren zaman lafiya da warware rikice rikice na zangon karatu na shekarar 2020, inda nake sa ran samun digiri na uku a shekarar 2023.” Inji Onoja.

Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta
Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta
Asali: UGC

“Duniya na bukatar samun kwararrun masu warware rikici rikicen daka tasowa a kowanne lokaci, ina fatan zama guda daga cikin wadannan kwararru a cikin shekaru masu zuwa. Ina fatan nan da shekara 4-5 zan kammala digirin PhD, a yau muka fara.” Inji shi.

Onoja mai shekaru 45 ya karanci ilimin kimiyyar kasa da ma’adanan kasa ne a jami’ar Jos a shekarar 1999, shi ne tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Kogi a zangon mulkin Gwamna Yahaya Bello na farko, sa’annan ya zama mataimakin gwamna bayan majalisar dokokin jahar ta tsige Simon Achuba.

Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta
Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta
Asali: UGC

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bara game da zargin da ake yi masa da hannu cikin badakalar kudin makamai a zamanin da yake minista, sa’annan ya wanke manyan hadimansa guda biyu, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje.

A makon nan ne wasu rahotanni daga jaridu daban daban suka bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kaddamar da bincike a kan badakalar kwangilar sayo makamai da aka yi a ma’aikatar tsaro a shekarar 2008.

Sai dai jaridar Kwankwaso ya kasance ministan tsaro ne daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2006, kamar yadda tsohon gwamnan ya tabbatar da kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel