Coronavirus: Za a dakatar da zaman Majalisar Wakilai na tarayya tsawon makonni biyu

Coronavirus: Za a dakatar da zaman Majalisar Wakilai na tarayya tsawon makonni biyu

- 'Yan majalisar tarayyar Najeriya sun bukaci a rufe majalisar na tsawon makonni biyu

- 'Yan majalisar sun ce za su yi amfani da wannan lokacin du duba irin shirin da gwamnatin tarayya ta yi a kasar

- A halin yanzu dai, an amince da bukatar dage zaman majalisar na tsawon makonni biyun

Majalisar Wakilai na tarayya za ta dage zamanta na tsawon makonni biyu saboda fargabar yiwuwar yaduwar cutar Coronavirus a Majalisar ta tarayya.

Majalisar ta cimma matsayar dakatar da zamanta ne bayan da Mista Josiah Idem ya gabatar da bukatar yin hakan a zauren majalisar a ranar Talata kuma sauran takwarorinsa suka amince da hakan.

Shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu, ya kara neman a dakatar da zaman majalisar na makonni biyu domin a bawa masana lokaci su shirya wa cutar a harabar Majalisar na Tarayya.

Ahmed Nasir ya bayyana damuwarsa a kan rashin isasun wuraren gwaje-gwajen cutar a Najeriya idan an samu barkewar cutar. Shi kuma Honarabul Sununu ya yabawa hukumar NCDC saboda shirin da ta yi cikin hanzari na gwajin cutar da kebe wanda ke dauke da ita a Najeriya.

DUBA WANNAN: Hana bara a Kano: Halin da almajirai suka shiga

Wannan bukatar ta samu amincewar majalisar baki daya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel