Da duminsa: Kotu Koli ta tafi hutun rabin lokaci, za ta dawo karfe 3 domin yanke hukunci kan shari'ar zaben Imo

Da duminsa: Kotu Koli ta tafi hutun rabin lokaci, za ta dawo karfe 3 domin yanke hukunci kan shari'ar zaben Imo

Kotun kolin Najeriya ta dakatad da zaman sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Imo inda tsohon gwamna, Emeka Ihedioha, ya bukaceta ta sake duba hukuncin cireshi daga kujeraran gwamna.

Kwamitin Alkalai bakwai karkashin jagorancin CHN, Ibrahim Muhammad Tanko, sun tafi hutun rabin lokaci ne byan sauraron bayanan bangarorin biyu kuma zasu dawo misalin karfe 3 domin yanke hukunci.

Lauyan Ihedioha da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Kanu Agabi (SAN), ya bukaci kotun ta lashe amanta da tayi ranar 14 ga Junairu na kwace kujerar gwamnan PDP da baiwa Hope Uzodinma na APC.

Shi kuwa lauyan Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Damina Dodo SAN ya bukaci kotu tayi watsi da bukatar PDP saboda basu da wani kwakkwarin hujja.

Ya kara da cewa dalili daya kacal zai iya sa kotun koli ta canza shari'ar da tayi kuma shine idan anyi tuntuben alkalami wajen rubuta shari'a.

Kotun ta cika da lauyoyi da yan siyasa na PDP da APC.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman sune shugaban APC, Adams Oshiomole da Uche Secondus na PDP.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel