Matata mazinaciya ce, a rabu mu har abada: Fasto ya fadawa kotu

Matata mazinaciya ce, a rabu mu har abada: Fasto ya fadawa kotu

Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Igando a Legas a ranar Litinin ta raba aure tsakin wani Fasto mai shekaru 47, Gbenga Aina da matarsa Damilola a kan zargin aikata zina.

Shugaban kotun, Mista Adeniyi Koledoye a yayin yanke hukuncin ya ce bisa ga dukkan alamu ma'auratan sun gaji da zaman auren.

Ya kuma ce duk kokarin da aka yi na sulhunta su ya ci tura.

Koladoye ya ce, "Tunda bangarorin biyu sun amince a raba auren, wannan kotu ba ta da wani zabi ila a raba auren."

"Kotu ta raba aure tsakanin Mista Gbenga Aina da Mrs Damilola Aina a yau. Daga yanzu ba matsayin mata da miji ku ke ba."

Matata mazinaciya ce, a rabu mu har abada: Fasto ya fadawa kotu
Matata mazinaciya ce, a rabu mu har abada: Fasto ya fadawa kotu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta ruwaito cewa Koledoye ya ce Gbenga ne zai dauki nauyin ciyar da yaransu uku da karatunsu da walwalarsu.

Wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa matarsa mazinaciya ce.

Ya ce, "Matata tana zina da wani mutum mai suna Shola".

"Wasu lokutan Shola ya kan kira ni a waya ya fada min cewa matata ta zama tashi kuma in manta da ita.

"Da na gudanar da bincike na gano cewa shi da matata suna zuwa coci guda kuma sun dade suna soyyaya.

"Ina rokon kotu ta raba aurenmu; Bana kaunar ta kuma, na auri wata matar," in ji shi.

Damilola ta yi ikirarin cewa mijinta ne ya kore ta daga gidansa.

Ta ce, "Gbenga ya kore ni daga gidansa, ya yi barazanar zai min duka idan na sake dawowa hakan yasa ban koma ba."

"Ba na zina da Shola kamar yadda ya yi ikirari. Kawai da muna mutunci ne kuma yana taimaka min wurin samun izinin fita kasar waje.

"Tun farko ba jin dadin auren na ke yi ba. Kullum rikici mu ke yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel