'Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Kano, sun raunata wasu hudu

'Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Kano, sun raunata wasu hudu

Wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba a daren ranar Litinin sun kai hari a garin Bagwai da ke karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano inda suka kashe mutane biyu tare da raunata wasu mutanen hudu.

The Nation ta gano cewa wadanda ake zargin 'yan bindigan ne sun isa garin ne a cikin mota misalin karfe 10.30 na dare inda suka kashe dan wani jigo a jam'iyyar PDP a garon da wata shugaban shiyya na PDP a Kano ta Arewa, Hajiya Balaraba Sani.

An kuma gano cewa sun kashe wani matashi mai suna Muhammad dan shekara 35 ma'aikacin sashin lafiya na karamar hukumar Bagwai yayin harin.

'Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Kano, sun raunata wasu hudu

'Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Kano, sun raunata wasu hudu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

Majiyar ta ce lamarin ya faru ne a gaban shagon wasu masu sayar da kifi a garin inda mutane ke taruwa su shakata.

An bayyana cewa daga bisani 'yan sanda sun iso sun kwashe gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Jami'in labarai na karamar hukumar Bagwai, Shibili Rabiu ya tabbatar da afkuwar lamarin unda ya ce mutum daya daga cikinsu ya mutu nan take, yayin da dayan ya mutu a asibitin su kuma sauran suna karbar magani.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ba ta fitar da wani sanarwa game da afkuwar lamarin ba a lokacin da ake hada wannan rahoton.

A baya, mun kawo muku cewa daya daga cikin wadanda shari’ar Musuluncin ta ritsa da shi mai suna Lawalli Isa, wanda aka datse wa hannun dama a 2001 a kan satar keke da ya yi, ya bayyana matsayarsa a kan yadda lamarin ya shafi rayuwarsa.

A zantawar da jaridar The Punch ta yi da shi, ta tambaye shi yadda yake rayuwa bayan an datse masa hannu ta sanadin shari’ar Musulunci a jihar. Lawalli ya ce, “Ba ni kadai aka cire wa hannu ba a wannan lokacin. Ni ne na biyu a jihar kuma na karshe.

Lawalli ya bayyana cewa, an kama shi ne da keken sata kuma ya amsa laifinsa a gaban kotun. Bayan amsa laifinsa ne mai shari’ar yace ko ya san hukuncin sata a Musulunci, ya kuma amsa da ya sani. Bayan yanke hukuncin ne aka tambayeshi ko zai daukaka kara amma sai yace ya hakura zai karba hukuncin Allah.

A ranar 1 ga watan Maris na 2001 ne aka tsinke masa hannun damansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel