Kasar Argentina ta zama kasa ta farko a duniya da ta halatta zubar da ciki
- Kasar Argentina ta shiga cikin tarihi inda ta bayyana kasa ta farko a Latin America da ta fara halasta zubar da ciki
- A kasar Argentina, an halasta zubar da ciki idan fyade aka yi wa mace ko kuma cikin zai zama barazana ga lafiyar mahaifiyar
- A yankin da yawancin mabiya addinin Kirista ne kuma darikar Katolika, kasashen Cuba da Uruguay ne kadai suka halasta zubda ciki
Kasar Argentina ta shiga cikin tarihi inda ta bayyana kasa ta farko a Latin America da ta fara halasta zubar da ciki.
A kasar Argentina, an halasta zubar da ciki idan fyade aka yi wa mace ko kuma cikin zai zama barazana ga lafiyar mahaifiya. Amma a halin yanzu, shugaban kasa Alberto Fernandez ya tabbatar da cewa zai mika bukatar halasta zubda cikin ga duk wacce tayi ra'ayi a gaban majalisa nan da kwanaki 10.
"Dole ne kasar nan ta bada kariya ga kowa da kuma mata," ya ce a jawabin shi na taron farko na wannan shekarar a daren Lahadi.
"Akwai bukatar al'ummar karni na 21 su mutunta ra'ayin jama'a sannan a basu 'yancin amfani da jikinsu yadda suke so." yace.

Asali: Getty Images
KU KARANTA: Tirkashi: Na kama mata ta na zina da wani kato a dakin otel - Ahmed Salisu
Idan aka tabbatar da bukatar, Argentina za ta zama kasa ta farko a yankin da ta fara aminta da zubar da ciki.
A yankin da yawancin mabiya addinin Kirista ne kuma darikar Katolika, kasashen Cuba da Uruguay ne kadai suka halasta zubda ciki.
Idan zamu tuna a 2018, dokar iya zubda ciki a cikin makonni 14 na daukar cikin ta samu aminci amma sai majalisar dattijan kasar tayi watsi da ita. Amma kuma a halin yanzu akwai rahotanni da ke bayyana cewa wannan dokar za ta samu aminci a majalisa don shugaban kasar ne ya mika.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng