Tashin hankali: Wani mutumi ya yiwa direban mota naushi daya kacal ya mutu
- Wani direban tasi ya sheka lahira bayan fadan da suka yi da wani mamallakin mota kirar Lexus SUV
- Lamarin ya faru ne a shataletatalen Warehouse da ke Owerri a babban birnin jihar Imo da ke yankin kudancin Najeriya
- Direban tasi din ya bugi motar kirar Lexus SUV wacce matashin ke tuki, amma sai matashin ya fito a fusace tare da naushin matukin
Wani direban tasi ya sheka lahira bayan fadan da suka yi da wani mamallakin mota kirar Lexus SUV.
Ganau ba jiyau ba, sun zargin mai motar da yi wa mai tasin mugun duka bayan sun ci karo. An gano cewa lamarin ya faru ne a shataletalen Warehouse da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.
Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, lamarin ya faru ne Owerri inda direban tasi ya bugi motar kirar Lexus SUV. Mai motar kuwa matashi ne mai jini a jiki wanda ya fito daga motar da gaggawa sannan ya fara dukan direban tasin. Lamarin da yasa ya fadi kasa a mace.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Tirkashi: Na kama mata ta na zina da wani kato a dakin otel - Ahmed Salisu

Asali: Twitter
A wani labari na daban kuwa, wani malamin addinin Musulunci mai suna Ahmed Salisu ya koka a gaban kotu a kan yadda ya kama matar shi tare da wani kato.
Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce kotun ba ta da wani dabara daya wuce ta tsinke igiyar aurensu din tunda mai karar ya matsanta a kan saki bayan mutane da yawan da suka saka baki.
“A don haka ne kotun ta tsinke igiyar auren da ke tsakanin Ahmed Salisu da Fatima Salisu. Daga yau dukkanku kun tashi daga ma’auratan juna. Kowannenku zai iya rayuwarshi ba tare da tsangwama ko hantarar juna ba. Kotun na muku fatan alheri.
“Wanda yayi karar zai biya tsohuwar matar tashi N150,000 don ta ci gaba da rayuwarta.” Koledoye yace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng