A karon farko wani Farfesan Najeriya ya bayyana cewa ya samo maganin Coronavirus dana zazzabin Lassa

A karon farko wani Farfesan Najeriya ya bayyana cewa ya samo maganin Coronavirus dana zazzabin Lassa

- Wani farfesa dan Najeriya mai suna Farfesa Maduike Ezeibe ya sanar da cewa ya samo maganin cutar Coronavirus da zazzabin Lassa

- Farfesan a fannin 'Virology' a jami'ar Michael Okpara ta aikin noma da ke Umudike, ya taba ikirarin samo maganin cuta mai karya garkuwar jiki

- Azeibe ya yi kira ga kasashen duniya da muguwar cutar ta addaba a kan su gwada maganin shi a kan marasa lafiyan

Wani farfesa dan Najeriya mai suna Farfesa Maduike Ezeibe ya sanar da cewa ya samo maganin cutar Coronavirus da zazzabin Lassa, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Farfesan a fannin 'Virology' a jami'ar Michael Okpara ta aikin noma da ke Umudike, ya taba ikirarin samo maganin cuta mai karya garkuwar jiki. Ya tabbatar da cewa tunda ya samar da maganin cuta mai karya gakuwar jikj, cutar Coronavirus za ta zama tarihi.

Azeibe ya yi kira ga kasashen duniya da muguwar cutar ta addaba a kan su gwada maganin shi a kan marasa lafiyan.

Idan za mu tuna, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta bada kudi tsaba har naira miliyan 36 ga duk dan Najeriyan da ya samo maganin cutar Coronavirus da zazzabin Lassa.

Cutar dai ta barke ne a kasar China inda ta kwashe rayuka 3,057 a fadin duniya tare da kayar da mutane 80,000.

A karon farko wani Farfesan Najeriya ya bayyana cewa ya samo maganin Coronavirus dana zazzabin Lassa
A karon farko wani Farfesan Najeriya ya bayyana cewa ya samo maganin Coronavirus dana zazzabin Lassa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tirkashi: Na kama mata ta na zina da wani kato a dakin otel - Ahmed Salisu

Gwamnatin tarayya ta sanar da bullar cutar ne a ranar Alhamis bayan wani dan asalin kasar Italiya ya zo Najeriya inda ya sauka a jihar Legas. Bayan ganowa da aka yi yana dauke da cutar, gwamnatin jihar Legas ta gaggauta samar da cibiyar gaggawa inda ta killace shi.

Kamar yadda gwamnatin ta sanar, yana karbar magani kuma sauki na samuwa.

Amma ba a nan gizo ke sakar ba, an fara bibiyar duk wanda ya yi wata mu'amala da dan kasar Italiya din. Daga nan ne aka samo sama da mutane 30 daga jihar Ogun don gwajin cutar.

Hakazalika, a jihar Filato an killace wasu 'yan kasar China hudu da suka nuna alamar cutar. Amma kuma gwamnatin jihar ta sanar da cewa gwaji ya nuna basu dauke da mugunyar cutar mai wa dan Adam kisan kiyashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng